Daga - Mahadi Tukur Almizan
Dakarun Amurka da Burtaniya sun kai hare hare kusan 900 daga watan January zuwa yau, a yunƙurin daƙile hare haren goyon bayan Palasɗinawa da Yemen ke kaiwa Isra'ila, sai dai Amurka da Burtaniyar ba su yi nasarar daƙile Yemen ba.
Kafafen yada labarai na ƙasar Yemen sun sanar da afkuwar wani sabon hari da jiragen Amurka da Burtaniya suka kai gundumar Bajil dake yankin Hodeidah a shekaranjiya Alhamis 28 ga watan Nuwamba, ƴan mintuna kaɗan bayan shugaban ƙungiyar Ansarullah ta Yemen Sayyid Abdul-Malik Al-Houthi ya kammala jawabi inda ya jaddada cewa Yemen zata cigaba da amfani da ƙarfin soji wajen nuna goyon baya ga al'ummar Palasɗinu.
"Ba zamu bari duka ɓangarorin dake yaƙar Isra'ila su rufe ba a ƙyale Gaza ita kaɗai, muna nan a filin daga domin goyon bayan Palasɗinu, da yardar Allah zamu yi duk abinda muke iyawa wajen goyon bayan al'ummar Palasɗinu". Wasu kenan daga kalaman Sayyid Abdul-Malik a ranar Alhamis
Ya ƙara da cewa "Cikakken ikon hana jigila zuwa Isra'ila a Red Sea na hannun mu, kuma wannan goyon bayan na nan babu ja da baya "
Hakanan Sayyid Abdul-Malik ya bayyana cewa Amurka da Burtaniya sun kai jimillar hare hare 844 da jiragen sama a kan ƙasa mafi talauci a cikin ƙasashen Larabawa, kuma wannan baisa mun canza matsayar mu ba, daga fara wannan yaƙi zuwa yanzu.
Washington da London sun ƙaddamar da yaƙi kan Yemen tun a watan January na wannan shekarar da nufin daƙile hare haren da Yemen ke yi domin goyon bayan Palasɗinu, saboda haka su kuma dakarun na Yemen suka ci gaba da kai ma jiragen yaƙin ƙasashen yamma hari da suka jibge a Red Sea, wanda a baya bayan nan dole tasa Amurka ta ɗauke babban jirgin ruwan nan mai ɗaukar jiragen yaƙi da ake kira "USS Lincoln Aircraft Carrier" daga ruwan yammacin Asia gaba ɗaya sakamakon hare haren na Yemenawa.
🇾🇪 Yemen Leader al-Houthi: "The USS Eisenhower fled the Red Sea, followed by the Abraham Lincoln, along with a third aircraft carrier... For the first time in the history of the U.S. Navy, aircraft carriers have lost their deterrence role since their use began.... The British… pic.twitter.com/qw60eXlppJ
— COMBATE |🇵🇷 (@upholdreality) November 28, 2024
"A karon farko a tarihin sojin ruwan Amurka, basuyi nasara ba a amfani da wannan babban jirgi wanda suka saba amfani dashi wajen É—aukar makamai da kai hare hare" cewar Sayyid Abdul-Malik
Shugaba na Ansarullah ya buɗe jawabin na shi na ranar Alhamis ne da shahararrun kalmomin da Shaheed Sayyid Nasrallah ya saba faɗi cewa "Lokacin rashi nasara ya ƙaura, lokacin nasara ya zo".
Sayyid Abdul-Malik yace "Burin maƙiya (Isra'ila) a Lebanon shine rusa rundunar Hezbollah da raba su da makamai, ta yadda zasu kawar da ƴan gwagwarmayar musulunci a Lebanon, ya zamanto jihadi baya da muhalli".
"Sai dai maƙiya ba su yi nasara ba, sun yi fatan haifar da matsaloli a cikin gida ta hannun Amurka ta hanyar siyasa , matsa sojin Lebanon domin su yi abinda zai amfanar da Isra'ila, daga karshe dai maƙiya sun tabbatar ba za su taɓa cimma wannan burin na su ba na ganin bayan Hezbollah " Waɗannan bayanai na Sayyid Abdul-Malik sun zo ne kwana daya bayan zartar da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka da Faransa suka jagoranta a Lebanon.
"Kariyar goben Lebanon za ta samu ne kawai ta hanyar muqawama, sojin ƙasa da kuma al'ummar Lebanon" abinda ya kira 'Three way equation.
Wannan tajdeedin matsaya na Ansarullah ya zo ne kwana É—aya bayan gamayyar rundunonin Æ´an muqawama na Iraqi (IRI) sun jaddada cewa za su cigaba da kai hare haren goyon baya ga al'ummar PalasÉ—inu.
