Daga - Mahadi Tukur Almizan
Ayarin motocin na ɗauke da magunguna da wasu kayan aikin lafiya da kuma man fetur, Isra'ila ta hari ayarin jim kaɗan bayan ta hari motocin 'World Food Programme' dake bada tallafin abinci.
Sojin na Isra'ila sun hari motocin kawo agajin ne ta hanyar amfani da jirgin yaƙi a jiya Alhamis 29 August, inda suka kashe mutum 5 na kamfanin sufurin dake jigilar kayan tallafin kamar yadda kafar yaɗa labarai ta 'The Guardian' ta wallafa a yau 30 ga watan na August.
Ayarin motocin na kungiyar 'Anera' na kan hanyar kai kayan agajin ne zuwa asibitin 'Emirati Hospital' dake Rafah, birnin dake kan iyakar Gaza da Egypt.
American aid organization Anera revealed that on Thursday, an Israeli airstrike targeted its aid convoy in Gaza, killing five Palestinian staff members.
— Quds News Network (@QudsNen) August 30, 2024
The convoy, which was delivering food and fuel to the Emirati Red Crescent Hospital, was coordinated with unarmed security… pic.twitter.com/KOAQ5461fu
Tun kafin tasowar motocin kungiyar ta shirya da Isra'ila cewa ba za su hari ayarin motocin ba.
Daraktan ƙungiyar ta Anera na kasar Palestine ya bayyana cewa " Wannan abu ne mai ban mamaki domin ayarin motocin na Anera ya samu yarjewar hukumomin Isra'ila tun farko, amma kuma gashi sun hari ayarin".
Daraktan mai suna Rasheed ya kara da cewa "An kashe jami'an kamfanin sufurin da suke aiki tare da su domin jigilar kayan tallafin wanda suke cikin motar farko ta ayarin".
Sai dai hukumomin sojin Isra'ila sun bayyana cewa tabbas akwai yarjejeniya tsakanin su da ƙungiyar ta Anera na wucewa da kayan tallafin, amma wai sojin Isra'ila sun yi kokarin dakile wani yunkurin wasu masu makamai ne da suka yi kokarin ƙwace ragamar ayarin motocin.
Ƴan awanni kafin wannan harin sojin na Isra'ila sun buɗe ma motar 'World Food Programme' (WFP) waɗanda motar ta su ke ɗauke da bajen majalisar ɗinkin duniya, sojin na Isra'ila sun harbi tagar motar da harsasai har guda goma yayin da take kusantar shingen bincike (Checkpoint) a unguwar Wadi Gaza.
Sai dai kasantuwar motar na da kariyar bullet, harsasan basu iya fasa gilashin motar ba, hakan yasa babu wanda ya mutu ko ya samu rauni a motar.
