Offline

A Cikin Wannan Makon Isra'ila Ta Kashe Aƙalla Palasɗinawa 20 A West Bank

A jiya ma jirgi maras matuƙi ya kai hari Jenin.

Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Mayaƙa uku daga ƙungiyar ƴan muqawama na Palasɗinawa ne suka yi shahada a harin da Isra'ila ta kai kusa da birnin Jenin dake West Bank a jiya juma'a 30 August.


Wannan ya biyo bayan arangama da aka samu tsakanin sojin Isra'ila da dakarun rundunonin muqawama a sansanin gudun hijira da unguwannin dake West Bank ɗin.


Kafar yaɗa labarai ta WAFA wallafa labarin dake cewa "Palasɗinawa uku Isra'ila ta kashe da safiyar jiya a wani hari da ta kai ta sama a Zababdeh dake kudancin Jenin".

An bayyana mutane ukun a matsayin Maysara Sulaiman Masharqa, Arafat Jaser al-Amer da kuma Wissam Ayman al-khazem, shi Wissam Khazem ɗin shine Kwamandan reshen  rundunar Qassam Brigade a Jenin, shi kuma Arafat ɗan rundunar Qud's Brigade ne ta kungiyar  Palestinian Islamic Jihad.


Hukumar lafiya ta Palasɗinawa ta bayyana cewa sojojin Isra'ila sun tafi da gawarwakin su.

Post a Comment

Previous Post Next Post