Offline

Wani Jariri Ya Kamu Da Cutar Shan Inna 'Polio' Sakamakon Watsuwar Cutar Da Rashin Riga-kafi Ya Haifar A Gaza

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan 

An samu cutar Polio a karon farko cikin shekaru 25 sakamakon gurbata ruwan zirin Gaza da Isra'ila ta yi.


Hukumar lafiya ta duniya 'WHO' ta tabbatar da cewa wani jariri É—an kimanin watanni 10 ya kamu da cutar shan inna, kuma wannan shine karo na farko a cikin shekaru sama da 25, shugaban hukumar agajin PalasÉ—inawa ta majalisar dinkin duniya 'UNRWA' Philippe Lazzarini ya bayyana a  jiya juma'a 23 August.

"Bai kamata a bari cutar shan inna 'Polio' ta banbance tsakanin Yaran PalasÉ—inawa da na Isra'ila ba" cewar Lazzarini a wata sanarwa da ya karanta a farkon gangamin da hukumar ta 'UNRWA' ta yi na neman a baiwa Yaran PalasÉ—inawa a Gaza riga kafin Polio ta hannun asibitocin 'WHO' da ma'aikatan su dake zagayawa.


Ya kara da cewa "Jinkirin samar da tallafin riga kafin zai yaÉ—a cutar a tsakanin sauran yaran PalasÉ—inawa"


"Bai wadata kawai a kawo riga kafi zuwa Gaza ba, domin samar da sauyi dole ne riga-kafin ya shiga bakin kowane Yaro daga Yaran PalasÉ—inawa wanda bai wuce shekara 10 ba" a cewar Lazzarini


Hukumar sojin Isra'ila mai kula da al'amarin fararen hular PalasÉ—inawa 'COGAT' ta sanar a makon da ya gabata cewa "Muna kokarin tallafawa da riga kafi" a cewar sojin sun fara yin riga kafin a tsakanin sojin na Isra'ila kuma wai suna kokarin ganin riga kafin ya shiga zirin Gaza.


Cutar ta Polio dai cuta ce mai haɗari dake yaɗuwa a cikin gurbataccen abinci ko ruwa, tafi kama yara ƴan tsakanin shekaru biyar, cutar tafi kashe ƙananan Yaran masu karancin shekaru sakamakon matsalar numfashi.


Tuntuni dai ma'aikatar lafiya ta Gaza ta yi gargaÉ—in yaÉ—uwar wannan cuta, sakamakon rashin riga kafi da kuma karancin wuraren kulawa da marasa lafiya.


 

Post a Comment

Previous Post Next Post