Daga- Mahadi Tukur Almizan
Hukumar kula da ƙananan yara ta majalisar ɗinkin duniya da ake kira 'UNICEF' ta bayyana adadin Yaran Palasɗinawa da suka samu raunuka sanadiyyar hare haren haramtacciyar ƙasar Isra'ila a Gaza, sannan kuma ta bayyana cewa akwai dubunnan yara a ƙarƙashin ƙasa da baraguzan gine gine suka danne a yankunan na Falasɗinawa.
Mataimakin shugaban UNICEF Ted Chaiban yayi karin bayani a jiya Laraba a zaman kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya akan ƙananan yara.
Put children first.
— UNICEF (@UNICEF) June 26, 2024
At the @UN Security Council, UNICEF’s @TedChaiban asks countries to protect children caught up in conflict around the world, as the number of grave violations against children hits a record high.https://t.co/8n5yOH6fsS
Chaiban ya bayyana cewa "Ƙananan Yara na cigaba da shan matsananciyar wahala" musamman a zirin Gaza inda kashe kashe da rushe rushe suka ta'azzara.
Chaiban ya kara da cewa suna da alƙaluman sama da yara 23,000 sun ɓata ko sun yi shahada, haryanzu ba a san matsayin su ba ko suna a raye ko a mace.
Jami'in na UNICEF ya ƙara haskama kwamitin masifar da ta rashin shigar kayan tallafi zuwa Gaza wanda ya ƙara ta'azzara rashin abinci ga yara "Bayan tsawon watanni 9 na wannan ƙazamin rikicin, UNICEF da wasu hukumomin agaji nata kokarin yadda za su iya tallafawa masu bukatar agaji" cewar Chaiban.
Chaiban yayi kora da a samu tsagaita wuta na din din din a Gaza ƙananan yara ke rasa rayukansu sakamakon masifar yunwar da aka ƙaƙaba ma zirin Gaza.
Wakilin Palestinu a majalisar dinkin duniya Riyad Mansour yayi magana a zaman kwamitin tsaron na majalisar ɗinkin duniya inda ya bayyana cewa haramtacciyar ƙasar Isra'ila ta kashe ƙananan yara a cikin ƴan watannin nan fiye da adadin Yaran da suka mutu a rikice rikicen da aka samu a duniya cikin shekaru 4 da suka gabata.
Ya yi ƙiyasin aƙalla yara 16,000 suka yi shahada yayin da wasu 21000 sun ɓata babu labarin su ko suna raye ko suma sun yi shahada.
Mansour ya bayyana cewa yanzu dai gaza ta zama ƙabari ga ƙananan Yara, yayi kira ga kwamitin ya gaggauta ɗaukar matakin dakatar da Isra'ila.
