Offline

Yara 10 Ke Rasa Ƙafafuwan Su Kowace Rana A Gaza - UNRWA

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

A jiya 25 ga watan June Philippe Lazzarini shugaban hukumar agaji da ayyuka ga Palasɗinawa ta majalisar ɗinkin duniya "UNRWA ya  bayyana rahoton munanan raunukan da yaran Palasɗinawa suka samu sakamakon Boma Boman Isra'ila a Gaza.


"Muna samu yara 10 a kowace rana da suka rasa ƙafa daya ko duka biyu bisa ƙiyasi" Lazzarini ya bayyana ma manema labarai a Geneva.


Hukumar ta UNRWA ta tattara bayanan ne daga hukumar kula da yara ta majalisar ɗinkin duniya"UNICEF", hukumar ta bayyana cewa akwai wannan adadin bai ƙunshi waɗanda suke rasa hannuwa ba, wanda suka adadi ne mai yawa".


Lazzarini ya kara da cewa "Yara Goma a kowace rana yana nufin yara 2,000 a cikin kwanaki 260 zasu rasa ƙafa sakamakon wannan ƙazamin yaƙin".

Hakanan kuma wata ƙungiya mai zaman kanta ta ƙasar Amurka "Save The Chily" sun ƙiyasta aƙalla yara 21,000 sun ɓace ɓat a wannan yaƙin na Gaza.


A ranar Litinin ɗin da ta gabata hare haren Isra'ila a Gaza sun yi sanadiyyar mutuwar mutum 37,626, kashi 75% na wannan adadin ƙananan yara ne da mata da tsofaffi, sama da yara 15,821 daga matattun duk Yara ne, hakanan mata 10,475 daga matattun duk mata ne.


Ƙasar Girka (Greece) ta nemi kasashen Turai su gaggauta ɗaukar mataki kan wannan musibar kuma su yarda su ƙarbi yaran Palasɗinawa domin a basu kulawa daga raunuka da suka samu.


Ministan harkokin wajen ƙasar ta Greece George Gerapetritis ne ya bayyana haka a makon da ya gabata inda ya bayyana cewa" Dole ne mu fuskanci wannan musibar, dole ne ƙasashen Turai su buɗe ƙofar karɓar yaran Palasɗinawa domin yi masu magani, hakanan a samar da mafita ga Yaran dake fuskantar bala'in yunwa da sauran matsaloli".


Gerapetritis ya yi magana da Firaministan Palestinu Mohammad Mustafa sannan ya nemi goyon bayan wasu ƙasashe domin fara wannan aiki.


A baya bayan nan dai ƙasar Colombia ta bayyana aniyar ta na karɓar Yaran Palasɗinawa da suka samu raunuka domin kulawa da lafiyar su.



A halin yanzu dai babban bala'in da al'ummar Gaza ke fuskanta shine masifar Yunwa, wadda ta kashe aƙalla yara 33 a ɗan tsakanin nan.


Daga ƙarshe Lazzarini ya bayyana cewa  hukumar UNRWA ta rasa samun tallafin da ya kamata ta samu wannan ne ya haifar da ƙarancin tallafin abinci da hukumar ke bayarwa, ya kara da cewa a halin yanzu suna da abinda zasu iya rabawa na tallafi zuwa ƙarshen watan August, suna bukatar dalar Amurka miliyan $140 domin kaiwa karshen shekara.

Post a Comment

Previous Post Next Post