Offline

Quds Brigade Sun Yi Ma Sojojin Isra'ila Kwanton Ɓauna : Sun Kashe Sun Raunata Adadi Mai Yawa

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Ƙazamin kwanton ɓaunae da ƴan gwagwarmaya na Palestinu suka shirya ma sojin Isra'ila ya bar adadi mai yawa na sojin Isra'ila da raunuka.


Hakanan wani Captain ɗin sojin Isra'ila ya mutu wasu mutum 16 kuma sun samu raunuka, hakan ya tilasta ma sojojin ficewa daga birnin Jenin.


Da yammacin ranar Laraba 26 ga watan da muke ciki na June sojojin suka fice daga birnin na Jenin bayan sun sha wuta daga hannun ƴan gwagwarmaya.



Bayan faruwar lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar Captain da raunata sojoji 16 Helicopter ya sauka ya kwashe masu raunukan daga wajen.


Ƴan gwagwarmayar sun binne IED a ƙasa zurfin kimanin meter ɗaya da rabi, sun yi wannan tarko ne ga gungun sojin Isra'ila na "Namer APC troop carrier" kamar yadda sojin na Isra'ila suka tabbatar.


Bayan fashewar wancan IED ɗin na farko ne wani gungun masu kai ɗauki na sojin Isra'ila suka nufi wurin suma wani IED ɗin ya tashi da su anan ne Captain Alon Sacgiu ya mutu sauran Team ɗin shi kuma suka samu raunuka.


Captain Alon Sacgiu shine Commander na "Kfir Brigade's Haruv Battalion Sniper Unit", yanzu dai Sacgiu sun isa jahannama.


Sashen dakarun gwagwarmaya na Palastinu "Jenin Brigade of Palestinian Islamic Jihad" da ake kira 'Quds Brigade" sun ɗauki alhakin wannan kwanton ɓauna a wata sanarwa da suka fitar.


A ranar 26 June ɗin ne dai dakarun sojin na Isra'ila suka afka birnin na Jenin suka yi mummunan rusau a 'Nazareth Street'.



Wakilin kafar yaɗa labarai ta WAFA ya labarto cewa motocin rusau na sojin Isra'ila sun ƙaddamar da mummunan rusau a 'Nazareth Street' ɗin, bayan haka ne ƴan gwagwarmaya suka fuskance su aka yi musayar wuta wanda har sojin na Isra'ila suka riƙa harba tear gas a bayan asibitin gwamnati na Jenin da kuma harbin motocin fararen hula da bullet me rai.


Kafar ta WAFA ta kara da cewa sojin na Isra'ila sun afka wani Pharmacy kusa da asibitin kuma sun kama mutane da dama.


An samu tsanantar musayar wuta tsakanin ƴan gwagwarmaya da sojin na Isra'ila a birnin na Jenin har zuwa lokacin da Quds Brigade ɗin suka shirya ma sojin na Isra'ila wannan hari da ya tilasta masu ficewa daga birnin.


Post a Comment

Previous Post Next Post