Sakamakon UAE ÆŠin Ta Haramta Ma Amurkar Amfani Da Kasarta Wajen Kai Hari A Gabas Ya Tsakiya.
Fadar tsaron Amurka wato Pentagon ta fara tattara jiragen yakin ta dake ƙasar haɗaddiyar daular Larabawa wadda aka fi sani da Dubai, ta fara tattare su zuwa Qatar inda za ta mayar da jiragen.
Hakan ya biyo bayan matakin da ƙasar ta haɗadɗiyar daular Larabawan ta ɗauka na haramtawa Amurka amfani da kasar ta wajen kai ma wata ƙasa ko wata kungiya hari a faɗin Gabas ta Tsakiya.
Hukumomin UAE ɗin sun da Amurka wannan mataki ne tun a watan February da ya gabata cewa ba za su sake yarje ma Amurka yin amfani da sansanin sojin sama na Al Dhafra dake ƙasar ba wajen kai ma Yemen ko Iraqi hari batare da sanar da su ba tun kafin lokacin kai harin, kamar yadda jaridar "Wall Street Journal" ta wallafa.
Wani jami'in hukumomin UAE ya sanar da jaridar cewa "Mun ƙaƙaba ma Amurka haramcin kaina Iraqi ko Yemen hari daga kasar mu", a cewar jami'in wannan mataki ne na kariyar kai wato suna kare kasar su ne daga faɗawa cikin rikicin da ba nasu ba.
Sansanin sojin da Amurka suke a ƙasar ta UAE shine Al Dhafra dake nisan kilomita 32 a kudu da babban birnin ƙasar Abu Dhabi.
Amurka ta bada umarnin fara jigilar jiragen na ta daga Dubai zuwa sansanin Al Udeid dake kudu maso gabashin babban birnin ƙasar Qatar wato Doha tunda ita Qatar bata saka masu wannan haramcin ba.
Wannan matakin dai ya na kara nuna cewa Amurka na ta samun matsala da ƙawayen ta na Gabas ta Tsakiya a kokarin su na kare kasashen su daga shiga rikicin dake tsakanin Amurka da Iran da ƙawayenta ganin cewa Amurka ba zata iya basu kariya ba.
Idan baku manta ba a watan da ya gabata ne kafar yaÉ—a labarai ta Middle East Eye ta kawo rahoto inda Saudiyya da Oman da UAE É—in suka haramta ma Amurka amfani da kasashen su wajen kai harin maida martani ga Iran bayan martanin da Iran ta mayar kan Isra'ila.


