Daga - Mahadi Tukur Almizan
Hukumomin ƙasar Misra mai maƙotaka da haramtacciyar Kasar Isra'ila sun kama tare da tuhumar Mutane aƙalla 120 bisa nuna goyon bayan al'ummar Palestinu da Isra'ila ke kashewa a Gaza a cewar wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama na ƙasar ta Misra.
Ƙungiyar a wani rahoto da ta fitar ƙungiyar "Egyptian Initiative For Personal Right" (EIPR) ta bayyana cewa lauyoyin kungiyar sun tsaya ma wadanda aka kama ɗin a lokuta mabanbanta har sau takwas a gaban kotuna, ta bayyana haka ne a wani rahoto a ranar Alhamis.
Kungiyar ta bayyana cewa mutum 90 daga cikin wadanda aka kama ɗin suna zaman jiran Shari'a ne.
Ko a ranar 30 ga watan Afrilun da ya gabata hukumomin sun kama wasu mazaje 5 a gidajen su dake Alexandria bisa ayyukan da suke gudanar wa na goyon bayan Palasɗinawa.
An gabatar da su a gaban kotu tare da Shadi Mohammed ana tuhumar su da laifin yunkurin kifar da gwamnatin ta Egypt ta hanyar ƙirƙirar ƙungiyoyin ta'addanci, wai saboda suna kiran tarurruka da shirye shirye a kafafen yada labarai.
Duka mutane shidan da aka gabatar a gaban kotu rahoton ya bayyana cewa suna zaman jiran shari'a ne.
Hakanan kuma an sake kama wasu mutane 6 ciki har da yara 2, bisa laifin sun yi rubutun nuna goyon baya ga al'ummar Palestinu a jikin gasar Dar el-Salam dake birnin Cairo.
Aƙalla mutum 28 ne aka kama a kusa da Tahrir Square a birnin na Cairo a ranar 24 da 25 Oktoban shekarar 2023 bayan kammala gagarumar zanga zangar nuna adawa da ta'addancin Isra'ila kan al'ummar Palestinu, an tsare waɗannan mutane karkashin dokar ta'addanci kuma ba a sanar da lauyoyin su ko ƴan uwan su ba.
Kwana ɗaya bayan wannan kuma an sake kama wasu mutum 11 bisa laifin sunyi musharaka a gangamin nuna goyon baya ga al'ummar Palestinu da ya gudana a kusa da Masallacin al-Azhar dake birnin na Cairo a ranar 27 Oktoba.
Rahoton na EIPR ya kara da cewa an sake kama wasu mutum 11 bisa laifin sun wallafa rubutun goyon bayan al'ummar Palestinu a kafafen sada zumunta.
Hakanan an sake kama wasu mutum 14 saboda sunyi musharaka a wata zanga zangar ta nuna goyon bayan Palasɗinawa a gaban Ofishin 'Journalist Syndicate' a birnin Cairo a farkon watan na Afrilu.
Hakanan an kama wasu mutum 19 wanda mafi yawancin su mata ne masu bincike, Lauyoyi, Ƴan Jarida da kuma ɗalibai an kama su bisa laifin sun yi musharaka a zanga zangar da ta gudana a wajen Ofishin 'United Nations' Women Headquarters' dake birnin na Cairo.
Hukumomin na kasar ta Egypt sun fara wannan kame kamen ne tun watan Oktoban da yaƙin ya barke a Gaza a cewar Rahoton na 'EIPR'.
Ƙungiyar ta yi kira ga hukumomin na kasar ta Misra su gaggauta sakin mutanen da suka kama sannan kuma su baiwa al'ummar ƴancin su na bayyana ra'ayoyin su ba tare da tsangwama ba.


