Offline

Membobin Ƙungiyar Vanguard Of Liberation Sun Kashe Jami'in Ƙungiyar Leƙen Asiri Ta Isra'ila " Mossad " A Misra.

Daga - Mahadi Tukur Almizan

An harbe wani jami'in ƙungiyar leƙen asiri ta haramtacciyar kasar Isra'ila da yayi ɓadda kama a matsayin ɗan kasuwa.

An harbe shi har lahira ne a birnin Alexandria na kasar ta Misra (Egypt).

Kafar yaɗa labaran kasar Isra'ila mai suna "KAN" ta sanar da kashe mutumin mai suna Ziv Kipper a ranar Talata.

Kipper yana basaja ne a matsayin shugaban kamfanin 'OK Group LLC' kamfanin dake shigo da ƴaƴan itatuwa da ganyayyaki (Fruits and Vegetables) zuwa kasar ta Misra babban Ofishin kamfanin yana birnin na Alexandria, sannan kuma suna da wasu Ofisoshin a Isra'ila da Ukraine.


Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta tabbatar da cewa mutumin ɗan asalin ƙasar Canada ne.


Kafar yaɗa labaran Isra'ila ta Ynet ta bayyana cewa mutumin ya shiga Misra ne da Passport ɗin Canada.


Wata ƙungiya mai suna "Vanguards Of Liberation" kungiyar Shaheed Muhammad Salah sun dauki alhakin kashe mutumin a wata sanar da suka yaɗa a kafafen sada zumunta.


Ƙungiyar ta bayyana cewa ta kashe wani  jami'in Isra'ila  a cewar su yana basaja ne da sunan kasuwanci amma a zahirin gaskiya jami'in Isra'ila ne da yake aikin tattara bayanai kuma yake horar da wasu ƴan ƙasar suna yi ma "Mossad" aiki.


Shaheed Muhammad Salah da kungiyar ke danganta kan ta da shi, shi dai jami'in sojan Misra ne mai kimanin shekaru 23 a duniya ya kaddamar da hari kan jami'an Isra'ila a ranar 08 ga watan October na shekarar da ta gabata wato bayan kwana ɗaya da Hamas ta kai ma Isra'ila hari, yayi nasarar kashe jami'an sojin Isra'ila uku a wannan hari na jarumta da ya ƙaddamar.



Post a Comment

Previous Post Next Post