Aƙalla jiragen ruwa dubu uku zasu yi fareti.
Daga - Mahadi Tukur Almizan
Dakarun sojin ruwa sun shirya faretin nuna goyon bayan al'ummar Palestinu a tashoshin jiragen ruwa.
Shugaban dakarun kare juyin juya hali na Iran wato IRGC Rear Admiral Ali Reza Tangsiri ya bada sanarwar cewa matuƙa jiragen ruwa na arewaci da kudancin Iran da adadin wasu tashoshin jiragen ruwa a faɗin duniya zasu gudanar da faretin nuna goyon baya ga Palestine A ranar 4 ga watan Afrilu da muka shiga.
Ali Reza ya bayyana haka ne a ranar juma'a da ta gabata, ya kuma bayyana cewa an shirya wannan faretin na jiragen ruwa dan nuna goyon baya ga al'ummar Palestine da kuma nuna fushi akan ta'addancin sahayuniyawa a Gaza.
"Faretin ruwan zai gudana ne duk a yunkurin Raya ranar Quds ta duniya dake tafe, Jiragen rundunar Basij ta dakarun ruwa na IRG zasu yi musharaka a wannan faretin hakanan ƙananan jirage daga kudanci da arewacin tekun Iran duk zasu yi musharaka, hakanan ma za a yi a wasu tashoshin jiragen ruwa a faɗin duniya. "
Ali Reza ya kara da cewa manya da ƙananan jiragen ruwa sama da 3000 ne zasu yi wannan fareti a Tekun Caspian da Gulf domin nuna goyon baya ga al'ummar Palestinu.
Ya kara da cewa jiragen ƴan Gwagwarmaya a Iraq, Syria, Lebanon da Yemen duk zasu yi musharaka a wannan faretin a ranar 4 ga Afrilu.
- Freedom Fighters NG



