- Mahadi Tukur Almizan
Jami'an ƴan sandan ƙasar Malaysia sun cika hannu da wani ɗan Isra'ila ɗauke bindugu har 6.
A ranar juma'a ne ƴan sandan suka sanar da kama mutumin wanda ya shiga ƙasar domin kashe wani mutumin Isra'ila ɗin, rahoton ƴan sanda ya nuna cewa an kama mutumin da bindugu 6 da harsasai 200.
Shugaban ƴan sandan Malaysia Tan Sri Razarudin Husain ya bayyana cewa an kama mutumin ne bayan sati biyu da shigowar shi ƙasar ta Malaysia.
Mutumin ya shigo ne ta tashar jirgin sama ta Kuala Lumpur, an kama shi a Jalan Ampang Hotel.
Hukumomin ƙasar sun bayyana cewa a lokacin da ake gudanar da bincike akan mutumin ya bayyana cewa ya shigo Malaysia ne da Fasfo (Passport) ɗin ƙasar Faransa da aka zurfafa bincike kuma an samu da Fasfo ɗin Isra'ila ya shigo.
Mutumin ya bayyana cewa ya shigo Malaysia ne domin ya kashe wani ɗan Isra'ila sakamakon faɗan dangi dake tsakanin su, sai dai jami'an tsaron sun bayyana cewa basu yarda da wannan iƙirarin nashi ba, sai dai kafafen yaɗa labarai na Malaysia sun bayyana cewa ana mutumin jami'in wata hukumar ƙila MOSSAD ko wata hukumar tsaro.
Shugaban ƴan sanda na Malaysia ya bayyana cewa mutumin ya sayi makamai ne ta hanyar amfani da Cryptocurrency, kuma ya bayyana cewa bayan ya sauka Malaysia ne ya siya waɗannan makamai.
Shugaban ƴan sandan ya bayyana cewa har yanzu muna tunanin bashi kaɗai yake aiki ba, akwai yiwuwar yana da abokan aiki da bamu kai ga gano su ba har yanzu, domin bincike ya nuna cewa a cikin sati biyun da yayi a ƙasar yaje wurare mabanbanta har uku.
- Freedom Fighters NG


