Offline

Muna da baƙaƙen ranaku a gabanmu - Cewar Shugaban Israel Military Intelligence Directorate General Aharon Haliva.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan


Shugaban Israel Military Intelligence Directorate mai suna General Aharon Haliva  yayi wasu zantuka ga wasu jami'ai a lokacin da suke yin meeting a ranar 4 ga wannan wata na April, inda ya bayyana masu cewa lallai zasu sha wahala a kwanaki masu zuwa.

Ga wasu daga cikin kalaman nasa " Masha faɗi maku cewa ba lallai bane ya zama abinda ya wuce shine mafi muni ba, domin kuwa baƙaƙen ranaku da zamu sha wahala suna gabanmu" waɗannan sune Zantukan General Aharon Haliva kamar yadda sojin na Isra'ila suka wallafa.

Wannan gargaɗin na General Haliva ga jami'an yazo rana ɗaya da maganar da mai magana da yawun Quds Brigades Abu Hamza yayi na alƙawarin nasara a kwanaki masu zuwa ga ƴan gwagwarmayar ƴanto Palsɗinu.


"Munyi maku alƙawarin nasara, kuma al'ummar Palestinu sai ta zama abun koyi ga dukkanin al'ummar duniya wajen juriya". Cewar Abu Hamza

"Ƴan gwagwarmaya zasu cigaba da fuskantar abokan gaba a Zirin Gaza,West Bank, Hakanan Lebanon zata cigaba da yaƙar ƴan mamaya a filin daga".

Tun farkon fara wannan yaƙi dai Hizbullah daga Lebanon, Islamic Resistance na Iraq (IRI) da Ansarullah na Yemen suke dafa ma ƴan gwagwarmayar Palestinu a cigaba da yaƙar Isra'ila, ta hanyar harar sansanonin sojin su har da jiragen ruwa a Red Sea.



Abu Hamza ya yi jinjina ga Hizbullah, ƴan gwagwarmaya na Iraqi da Ansarullah na Yemen da kuma uwa uba Iran.

Hakan kuma ya miƙa saƙon godiya ga al'ummar dake zanga-zangogin nuna goyon baya musamman na Jordan da wasu ƙasashen Larabawa.

- Freedom Fighters Ng

Post a Comment

Previous Post Next Post