Daga - Mahadi Tukur Almizan
Jami'an ƴan sandan jamhuriyar Musulunci ta Iran sunyi nasarar wargaza shirin ƴan ta'addan ISIS na kai hari lokacin Eidin ƙaramar Sallah dake tafe.
Iran dai ta zamo hadafin ƴan ta'adda masu tsattsauran ra'ayi a ƴan watannin nan.
Jami'an ƴan sandan sunyi nasara cafke ƴan ƙungiyar ta ISIS a a yau Asabar 6 ga watan Afrilu.
Sunyi nasara cafke wani babban jami'in na ISIS da wasu jami'an biyu da ake zargi da shirin kai hare haren ƙunar baƙin wake a lokacin bukukuwan Eidin ƙaramar Sallah dake tafe a ƙarshen wannan wata na Ramadan.
Babban jami'in na ISIS da ƴan sandan suka kama shine Mohammad Zaker wanda aka fi sani da "Ramesh" da sauran ƴan ta'addan a musayar wutar da ƴan sanda suka yi da su a yammacin babban birnin ƙasar ta Iran wato Tehran.
Kamun ya biyo bayan musayar wutar da jami'an rundunar "Jaish al-Adl suka yi da ƴan ta'addan na tsawon awanni 17 a ranar Alhamis wanda yayi sanadiyyar shahadar jami'an rundunar 10 da kuma mutuwar ƴan ta'addan 18.
Waɗannan ƴan ta'adda dai na samun goyon baya ne daga Amurka da Isra'ila, domin kuwa an daɗe ana zargin cewa Amurka da Isra'ila na amfani da ƴan ta'addan na ISIS da wasu ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi wajen kaima maƙiyan su hari har da Syria da Iraqi musamman a tsakanin shekarar 2013 da 2015.
Ko dai a watan da ya gabata wata ƙungiyar ƴan ta'adda reshen ISIS dake Afghanistan sun ɗauki alhakin mai hari birnin Moscow na Rasha, inda suka buɗe wuta da bindigu masu sarrafa kansu harbin kan mai uwa da wabi wanda yaci rayukan aƙalla mutum 144.
Hakanan kuma ƙungiyar ta ISIS ta ɗauki alhakin harin da aka kai a watan Janairun wannan shekarar inda aka kashe kusan mutum 100 a Iran yayin da ake taron tunawa da Shahadar Shaheed Qaseem Sulaimani a birnin Kerman wanda Amurka ta kashe a shekarar 2020.
- Freedom Fighters Ng
