Daga - Mahadi Tukur Almizan
Bayan Isra'ila ta kai hari wani bangare na Ofishin jakadancin Iran da ke Syria, ɗaya daga cikin rundunonin ƴan gwagwarmaya dake ƙarƙashin kulawar Iran da ake kira "Kata'ib Hezbollah " tayi iƙirarin kai harin maida martani ta hanyar baiwa mazaje makamai a Jordan.
Mai magana da yawun rundunar ta Kata'ib Hezbollah Abu al-askari ya ɗorama Isra'ila da Amurka alhakin wannan harin da yayi sanadiyyar shahadar Generals biyu na IRGC da wasu jami'an na IRGC biyar.
Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.fadakdata
Al-askari ya bayyana cewa rundunar Kata'ib zata baiwa mazaje ƴan gwagwarmaya mutum dubu goma 12 ƴan kungiyar "Mujahideen of the Islamic Resistance in Jordan" makamai manya da matsakaita da suka haɗa anti-armor launchers, tactical missiles, da miliyoyin rounds na alburusai da abubuwan fashewa, ya bayyana cewa zasu yi amfani da waɗannan makamai wajen tallafawa ƴan uwanmu PALASƊINAWA da kuma ɗaukar fansar waɗanda Isra'ila ta kashe mana.
Ga hoton takardar da Abul Askari ya ɗora a Group ɗin shi dake Telegram dake ɗauke da maganar ta sa 👇
Aikin Da Za Su Yi Idan kayan Aiki Sun Shiga Hannun su.
Wani abu mai haɗari a cikin maganar tasa ya bayyana cewa da zarar waɗannan makaman sun shiga hannun rijalan nan zasu datse bodar ƙasa dake tsakanin Isra'ila da Jordan madamar sun samu sahhalewa daga Hamas da Palestianian Islamic Jihad.
Manazarta da masu fashin baƙi sunyi ta sharhantar waɗannan kalamai da matakin na Kata'ib Hezbollah, inda wasu ke alaƙanta gagarumar zanga zangar dake gudana a ƙasar ta Jordan.
Idan baku manta ba a ranar 26 ga watan March anyi gagarumar zanga zanga wadda har jami'an ƴan sanda suka harba barkonon tsohuwa har da dukan masu zanga zangar yayinda suka yi yunkurin afkawa Ofishin jakadancin Isra'ila.
Hakanan a ranar 31 ga watan March ƴan fafutuka a Jordan ɗin sun gudanar da wata gagarumar zanga zangar nuna adawa da Isra'ila da neman a kawo karshen daidai tsakanin Jordan da Isra'ila.
Tun daga ranar 24 ga watan March dubban al'ummar Jordan ne ke fitowa zanga zangar a Ofishin Jakadancin Isra'ila dake babban birnin ƙasar Wato birnin Amman inda aka jibge jami'an tsaron kasar ta Jordan domin fuskantar masu zanga zangar.
Sai ƙungiyar Hamas da Muslim Brotherhood in Jordan sun yi ta karfafar wannan zanga zangar harma kwanakin baya kadan mai magana da yawun Hamas ya yi godiya ga masu zanga Zangar a Jordan inda ya ambace su musamman.
Kuma wani abu da ake kara duba akanshi shine akwai PALASƊINAWA a ƙalla 2.2 Miliyan a sansanonin ƴan gudun hijira na majalisar dinkin duniya dake Jordan ɗin kuma mafi yawan su sun zama ƴan ƙasar Jordan a hukumance.
Kamar yadda hoton dake kasa na shafin hukumar 👉united nations relief and works agency for palestine refugees in the near east
Wadannan abubuwan la'akarin ne suka sa ake ganin maganar Abu al-Askari tana bisa hanyar tabbata duba da yadda al'ummar ƙasar suka gaji da hukumomin ƙasar.
Sai dai kafar yaɗa labarai ta Assharƙ Al-awsaɗ (Asharq Al-Awsat) ta bayyana cewa ƙasar Iraki tayi watsi da wannan sanarwar ta Kata'ib Hezbollah, duba da cewa dokar kasar Iraqi bata amince ma wata ƙungiya ta baiwa wasu makamai ba a kasashen ketare domin gudanar da wani aiki, sun kara da cewa Iraqi ba zata amince da karya dokokin kasa da kasa ba musamman ga wadanda suke maƙotaka da su wato Jordan kenan.
Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.fadakdata
©️ Freedom Fighters Ng




