Saƙon Sayyid Nasrallah Dangane Da Ranar Quds Mai Zuwa.
- Daga Mahadi Tukur Almizan
Sakatare Janar na ƙungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah yayi kira ga al'ummar duniya su bunbunto suyi musharaka a ranar Quds dake tafe a juma'a mai zuwa.
Sayyid Nasrallah yayi waɗannan zantuka ne yayin da yake jawabi ta Talabijin ga mahalarta raya daren Lailatul Qadr dake kudancin Beirut babban birnin Lebanon a ranar juma'a 29 ga watan nan na March.
"Wannan shekarar Ranar Quds tazo da banbanci kuma al'amura sun ta'azzara" cewar Nasrallah
Yayi kira ga al'umma musamman na kudancin Lebanon su fito ƙwai da ƙwarƙwata domin raya wannan rana ta Quds
Kasancewar lokacin da yake magana lokaci ne na raya daren Lailatul Qadr, Sayyid Nasrallah ya nuna muhummanci addu'a sosai a yanayin da ake ciki.
Nasrallah ya ƙara da cewa" Kisan da ake yi kullum, rushe rushe, yunwa da raba mutane da Muhallansu dake faruwa kan al'ummar Gaza, a ɗaya bangaren kuma jajircewar ƴan Gwagwarmaya a fagen fama da juriyar al'ummar Gaza, duka waɗannan ya kamata su nuna mana buƙatuwar muyi addu'a "
"Abinda yake faruwa da mu a Kudancin Lebanon da hare haren da yaƙin da ke faruwa a Yemen, Syria, Iraq, da matsin tattalin arziki da ake fama dashi, suma ya kamata su zame mana ƙwarin gwuiwar yin addu'a, muna buƙatar addu'a domin duk sanda muka kai hari Allah yana bamu nasara." a cewar Sayyid Nasrallah kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Lebanon Al'ahed ta labarto.
Ana ganin wadannan kalamai na Sayyid Nasrallah dake ƙarfafa janibin addu'a a matsayin matakin daƙile farfagandar Maƙiya ta cewa kiran ayi addu'a kamar nuna raunin ƴan Gwagwarmaya.
Sayyid Nasrallah ya bayyana cewa addu'a tana da muhimmaci a lokacin ƙunci da walwala.
- Freedom Fighters NG

