- Mahadi Tukur Almizan
Kotun hukunta Duniya (International Court Of Justice) ta sanar da sababbin matakai dake baiwa Isra'ila umarnin tabbatar da shigar kayan tallafi zuwa Gaza ba tare da haifar da jinkiri ba.
Wannan umarni ya fito ne a ranar Alhamis makon i biyu bayan ƙasar Afirka ta kudu (South Africa) ta nemi kotun ta kara & daukar wasu matakai akan haramtacciyar ƙasar ta Isra'ila domin daƙile mummunan yanayin yunwa da ake fama dashi a Gaza.
A shekarar da ta gabata ne dai ƙasar ta Afirka ta Kudu ta kai ƙarar Isra'ila kotun duniya tana mai tuhumar ta da aikata kisan kare dangi kan al'ummar Palestine a Gaza.
A cikin watan Janairun wannan shekara kotun ta Duniya ta yi hukuncin wucin gadi, inda ta dauki mataki daidai yadda ƙasar Afirka ta kudu ta buƙata na cewa Isra'ila ta tabbatar ta ɗauki dukkanin matakan kauce ma aikata kisan ƙare dangi a Gaza.
A shekaranjiya Alhamis ICJ ta bayyana cewa "Dole ne Isra'ila ta bari a shiga da kayan tallafi batare da jinkiri ba".
Tun 26 Ga watan Janairun da ya gabata al'ummar Palestinu suka shiga matsanancin halin rayuwa a zirin Gaza musamman matsalar rashin abinci da sauran abubuwan buƙatu na yau da kullum a cewar ICJ
Daga cikin matakan da ICJ ta ɗauka akan Isra'ila harda cewa bazata tare hanyoyin shiga da tallafi zuwa Gaza ba, hakanan kotun ta buƙaci Isra'ila ta ƙara adadin hanyoyin shiga da tallafi Gaza gwargwadon buƙata.
Har wala yau kotun ta buƙaci Isra'ila ta gaggauta tabbatar da sojojin ta basu ci gaba da aikata ayyukan taka hakkokin al'ummar Palestinu ba a Gaza duk a kokarin kauce ma kisan kare dangi.
Kotun bayyana cewa dole ne Isra'ila ta miƙo rahoton matakan da ta ɗauka na bin Umarnin kotun da ta wajabta ma Israila , kotun ta baiwa Isra'ila wata ɗaya daga ranar da ta bayyana waɗannan matakai a matsayin wa'adin miƙo wannan rahoto.
Majalisar dinkin duniya da wasu hukumomi sunyi ta gargaɗin cewa za a shiga matsanancin halin yunwa sakamakon hana shiga da tallafi da Isra'ila tayi zuwa Gaza.
- Freedom Fighters NG


