Offline

Ƴan Gwagwarmaya Na Cigaba Da Kai Sojojin Isra'ila Jahannama, A Ƴan Kwanakin Abun Ya Girmama.

 


- Mahadi Tukur Almizan 


Isra'ila na cigaba da tafka a sarar rayuka a fagen fama duk da iƙirarin nasara da Netanyahu yake


Mayaƙan gwagwarmaya sun ƙara ƙaimi musamman a ƴan Kwanakin nan, inda suka kai zafafan hare hare mabanbanta da suka ci rayukan sojojin Isra'ila a kudu da kuma arewacin Gaza.


Wani hari ɗaya tamkar dubu da suka kai kan sojojin na Isra'ila a jiya juma'a 29 ga wata yayi ma sojojin mummunar ta'asa inda aka kwashi masu raunuka da yawa.


Kamar yadda zaku gani a cikin wannan faifan bidiyon da ya karaɗe kafafen labarai musamman na Yahudawa anga jirage na sauka a asibitocin Isra'ila suna sauke waɗanda harin ya rutsa dasu matattu da masu raunuka .


A ƙalla helicopter 5 ne suka yi jigilar sojojin da harin ya rutsa dasu zuwa asibitoci mabanbanta a jiya juma'a kamar yadda kafar yaɗa labarai ta The Cradle ta wallafa.


Ƴan Gwagwarmaya tsagin "Qassam Brigade" sun bayyana cewa sun yi nasarar harar gungun sojojin mamaya a wani gida kusa da asibitin Nasser da wani makami da ake kira "Anti-Fortification TBG Shell" wanda yayi sanadiyyar kashewa tare da raunata sojojin mamayar, wannan ne ya sabbaba saukar jiragen domin kwashe matattun sojojin da masu raunuka a yankin dake kudancin  Khan Yunis (Kudancin Gaza) a cewar Qassam Brigade. 



Cibiyar bincike da koyon yaƙi dake washington (Washington based institute for the study of war) a ranar Alhamis 28 ga wata ta bayyana cewa daga lokacin da Isra'ila ta ƙaddamar da hari kan asibitin Al-shifa a arewacin Gaza Qassam Brigade da sauran ƴan Gwagwarmaya sun kai hare hare sama da 70 akan sojojin Isra'ilar a yankin asibitin.


- Freedom Fighters NG

Post a Comment

Previous Post Next Post