Offline

Wannan Litinin Ɗin Itace Rana Mafi Muni A Tarihin Isra'ila - Sayyid Nasrallah.

 


Sayyid  Hassan Nasrallah ya kira ranar Litinin ɗin da ta gabata a matsayin Litinin mafi muni a tarihin haramtacciyar ƙasar Isra'ila, sakamakon antayawa cikin tashin hankali da ƙasar tayi a dalilin amincewa da ƙudurin farko na sauya fasalin dokoki da Netanyahu ya shigar.


A ranar 24 ga watan da muke ciki na Yuli, babban Sakataren ƙungiyar Hizbullah Sayyid Nasrallah ya bayyana cewa Isra'ila na kan hanyar rushewa sakamakon amincewa da ƙudurin farko na sauya fasalin dokoki da majalisar haramtacciyar ƙasar Isra'ila tayi wadda ake kira (Knesset).


A cewarsa "Wannan rana itace rana mafi muni a tarihin ƙasar Isra'ila, ko al'ummar Isra'ila zasu tabbatar da wannan batu nawa kuma wannan rana ce da Isra'ila ta hau kan hanyar hallaka gadan gadan" Nasrallah yayi wannan batu ne ta talabijin, ya ƙara da cewa "Insha Allah wannan shi zai kawo ƙarshen Isra'ila da ɗaiɗaicewarsu".


©️ Freedom Fighters Ng

   - Mahadi Tukur Almizan

Post a Comment

Previous Post Next Post