Elizabeth Tsurkov ta shiga ƙasar Lebanon na tsawon watanni uku, ba bisa ƙa'ida ba sakamakon haka jami'an tsaron ƙasar Lebanon sun duƙufa wajen gudanar da bincike domin gano waɗanda Tsurkov ta gana dasu a tsawon zaman cikin ƙasar.
Elizabeth Tsurkov dai tsohuwar Jami'ar soji ce ta ƙasar Isra'ila wadda tayi aiki a Intelligence Department, kuma a halin yanzu anyi garkuwa da ita a ƙasar Iraqi tun a watan March ɗin da ya gabata.
Hukumomin ƙasar Lebanon sun tabbatar da cewa Tsurkov ta shiga ƙasar su ba bisa ƙa'ida ba ta hanyar amfani da jabun fasfo ɗin ƙasar Rasha, kuma ta zauna a ƙasar har na tsawon watanni uku a tsakanin watan Afrilu da Yuli na Shekarar 2022.
Majiyar manema labarai ta bayyana cewa Tsurkov ta shiga ƙasar ta Lebanon ne da sunan "Elizaveta Tsurkova" wanda ya banbanta kaɗan da sunan da aka santa dashi ta hanyar amfani da fasfo ɗin ƙasar Rasha.
Jarida The Cradle ce dai ta fallasa labarin ɓatan wannan tsohuwar Jami'a a ƙasar Iraqi, yayinda suka samu bayanai daga jami'an tsaron ƙasar Iraqi a ranar 5 ga watan Yulin da muke ciki, bayan wasu awoyi da fallasa labarin sai Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fito yana zargin ƙungiyar ƴan Shi'a ƴan gwagwarmaya mai suna Kata'ib Hizbullah da aikata wannan ƙwamushe na tsohuwar Jami'ar su.
Tsurkov tayi aiki a rundunar sojin Isra'ila a Intelligence Department a lokacin yaƙin Hizbullah da Isra'ila a shekarar 2006 ta riƙa shiga ƙasar Lebanon da Iraqi da fasfo ɗin ƙasar Rasha, wanda hakan ya saɓa ma dokokin to ƙasashen biyu Iraqi da Lebanon, hakanan kuma dokokin ƙasashen biyu sun haramta ma duk wani ɗan ƙasar su mu'amala da ɗan Isra'ila.
Hakan yasa dai hukumomin tsaron ƙasar ta Lebanon suka duƙufa wajen gano mutanen da Tsurkov tayi mu'amala dasu a lokacin da ta kasance a ƙasar na watanni uku.
Tsurkov dai an haife ta a ƙasar Rasha daga baya sukayi hijira zuwa Isra'ila inda ta taso a haramtattun muhallan da yahudawa ke zaune a yammacin gabar kogin Jordan.
Tsurkov tayi ƙaryar cewa taje ƙasar Iraqi ne inda akayi garkuwa da ita domin gudanar da bincike kan Mabiya Muqtada Sadr na ƙasar ta Iraqi, wai wannan binciken yana da alaƙa da karatun da take a jami'ar Princeton (Princeton University).
©️ Freedom Fighters Ng
- Mahadi Tukur Almizan.
