Offline

Palasɗinawa Uku Jami'an Isra'ila Suka Shahadantar Jiya A Birnin Nablus.


©️ Freedom Fighters Ng

Wasu kafafen yaɗa labaraun cikin gida na Palasɗinawa sun bayyana cewa jami'an tsaron haramtacciyar ƙasar Isra'ila sun kashe Palasɗinawa Uku.


Jami'an haramtacciyar ƙasar ta Isra'ila sun harbi Palasɗinawan uku ne da bindiga a jiya Litinin 25 ga watan Yuli, a Yammacin Gabar Kogin Jordan a birnin Nablus da Isra'ilar ta mamaye , kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta Palasɗinawa ta bayyana ma manema labarai.


Anharbi mutanen uku duka da harsasan Isra'ila ma'aikatar lafiyar ta Palasɗinawa ta bayyana sunayen su kamar haka:

Nour Al-Din Al-Areda mai shekaru 32

Muntasir Salameh mai shekaru 33 da kuma

Sa'ad Al-kharraz mai shekaru 43.


Sai dai Jami'an tsaron Isra'ila sun bayyana cewa wata mota ɗauke da mayaƙa uku ɗauke da makamai sun buɗe ma sojojin su wuta a yayin da suke rangadi a Birnin Nablus, hakan yasa suma suka mayarda martani ta hanyar buɗe wuta.


Ita kuma gamayyar ƙungiyoyin gwagwarmaya na Palasɗinawa da suka haɗa da Hamas,Mujahideen da sauran bangarorin sun fitar da sanarwa wadda ta bayyana lamarin a matsayin arangama (Clashes).


Faruwar wannan lamari a jiya Talata, jami'an tsaron Isra'ila sun jibge sojojin a yankin.


Ko a kwanaki uku da suka gabata dai sojojin na Isra'ila sun kashe wani matashi ɗan shekara 18 a garin Sebastiya a yayin da yake  kan hanyar zuwa gida.


Post a Comment

Previous Post Next Post