Offline

Ƙoƙarin Murƙushe Guguwar Juyin Mulki A Afirka, Shugabannin Kasashen ECOWAS Sunyi Taro A Abuja.



©️ Freedom Fighters Ng


A cigaba da yunƙurin daƙile guguwar juyin mulkin soji da Afirka ke fuskanta a ƴan shekarun nan shugabannin kasashen ECOWAS sun gudanar da wani ƙwarya ƙwaryar taro a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.


Taron ya samu halartar shugaban ƙasar Nijeriya,Nijar da Guinea Bissau da Jamhuriyar Benin.


Shugabannin sun jaddada aniyar su ta ganin sun kawo ƙarshen duk wani yunƙurin juyin mulki, a cewarsu domin tabbatar da mulkin demokraɗiyya.


A yanzu da ƙasar Guinea da Mali da Burkina Faso suna ƙarƙashin mulkin soji sakamakon juyin mulki da sojoji sukayi a waɗannan ƙasashe.


Shugabannin sun ɗora ma shugaban jamhuriyar Benin Patrice Talon alhakin tuntuɓar sojojin da ke mulki a wasu ƙasashen Afrika domin ganin sun mayar da mulki hannun farar hula wato dai mulkin demokraɗiyya.


Hakanan kuma shugabannin na ECOWAS sun bayyana cewa zasu maye gurbin sojojin majalisar Ɗinkin Duniya da nasu a ƙasar Mali.


Ƙasar Mali ce dai ta nemi Majalisar Ɗinkin Duniya ta janye sojojin ta daga ƙasar bayan sun shafe shekaru batare da sun cimma hadafin kawo su ba, daga ƙarshe dai Majalisar Ɗinkin Duniyar ta yarda da buƙatar ta ƙasar Mali inda ta yarda da janye sojojin nata.

Post a Comment

Previous Post Next Post