Offline

Wasu Matasa Magoya Bayan Hizbullah Sun Ƙwamushe Kyamarar Tsaro Ta Isra'ila A Tare Da Musanya Tutar Isra'ila Da Ta Hizbullah.

 


Ɗaya Daga Cikin Kyamarorin Tsaro Mallakin Isra'ila Tayi Ɓatan Dabo A Bakin Bodarsu Da Lebanon.

Wata jaridar haramtacciyar ƙasar Isra'ila mai suna Hebrew Media ta wallafa a ranar 17 ga watan Yulin da muke ciki cewa an sace ɗaya daga kyamarorin tsaro na Isra'ila dake bakin bodarsu da Lebanon batare da sanin su ba tsawon awoyi.

Lamarin ya a auku ne a ranar Laraba 12 ga watan Yulin da muke ciki, a kusa da Mashigar  Fatima (Fatima's Gate) wadda ke tsakanin Lebanon da guraren da Isra'ila ta mamaye a cewar jaridar Israel's Channel 7.

Sojojin Isra'ila sun lura cewa an lalata sabon shingen bakin bodar, sama da awa 5 bayan ɓatan kyamarorin, sai dai anyi jinkiri wajen gudanar da binciken faruwar lamarin kamar yadda Hebrew Outlet ta ruwaito.

Jami'an da ke wajen basu san da ɓatan kyamarar ba akan lokaci sai dai daga baya sojojin sun rufe wasu anguwannin yankin domin gudanar da bincike ko jami'an hizbullah sun kutsa yankin.

Kwamandan sojin Isra'ila Major General Uri Gordin ya bayyana jinkirin gudanar da binciken a matsayin babban kuskure.

Ya kara da cewa bayan gudanar da tsattsauran bincike zamu dauki darasi daga abinda ya faru.

Tashar Talabijin ta Almanar ta bayyana cewa wasu matasa ne ƴan Lebanon masu goyon bayan Hizbullah suka cire kyamarar sannan kuma suka cire tutar Isra'ila suka musanyata da tutar Hizbullah.

Post a Comment

Previous Post Next Post