Offline

Iran,Rasha da Syria Suna Kokarin Tilasta Amurka Barin Ƙasar Syria.

 


A wani rahoto da wata kafar yaɗa labarai ta Al-monitor ta fitar a ranar 14 ga watan Yulin da muke ciki, ta ruwaito cewar anjiyo wani babban jami'in sojan Amurka yana faɗin cewa Ƙasar Rasha da Iran da Syria na wani gagarumin shiri wanda zai tilastama Amurka kwashe Sojojin ta daga ƙasar Syria.


Jami'in ya bayyana cewa  yaga alamar kwamandojin sojin ƙasar Rasha suna wani shiri a ƙarƙashin ƙasa tare da sojojin kare juyin juya halin Musulunci na Iran, wanda wannan shiri tsohon shiri ne na korar Amurka daga ƙasar ta Syria, cewar Al-monitor


Ya ƙara da cewa waɗannan ƙasashe uku Iran,Syria da Rasha suna da wani  ƙuduri da suka haɗu kanshi.


Ya ƙara da cewa dai wannan haɗakar ta samu tsari da haɗin kai da fahimtar juna ta yadda Iran da Rasha zasu bada gudummawar sojojin su.


Yace maganar gaskiya muma haka zamuyi, mu da ƙawayenmu akan wani abu da muke ƙoƙarin cimmawa, munga sunayin haka a ɓangarensu domin su tirsasamu mu gudu daga Syria".


A ƴan watannin dai Amurka tayi ta ƙara jibge dakarunta a ƙasar Syria a yankunan da ta mamaye musamman yankunan da ke da albarkatun mai.

Post a Comment

Previous Post Next Post