Wasu daliban jihar Osun dake kudancin Kwalejin kiwon lafiya ta jihar, sun samu munanan raunuka sakamakon harbin bindiga a shagon mai aski.
Lamarin ya faru ne a shagon wani mai aski a shataletalen Amuta dake ilesa, yayinda daliban sukaje kai cajin waya.
Maharan da suka bude wuta dai ana zargin 'yan kungiyar asiri ne dake zaune kusa da kwalejin.
Wata majiya ta bayyana ma manema labarai cewa Daliban da aka harba sun hada da mata biyu da namiji daya, baya faruwar lamarin angarzaya asibitin koyarwa ta jami'ar jihar ta Osun dake Osogbo, dasu domin basu kulawar likita.
Wata daliba da ta nemi a boye sunanta ta bayyana cewa "wannan harbin dai ya auku ne sakamakon fada tsakanin wasu kungiyoyin asiri dake adawa da juna"
"Kwatsam mukaji karar bindiga, sautin ya fito ne daga shagon mai askin da daliban sukaje kai chajin wayarsu, yayinda muka isa wajen domin ganin abinda ke faruwa, muntarar da namijin da aka harba daga cikinasu kwance cikin jini an harbeshi a ciki, shi kam ko a lokacin yariga ya mutu, inda su kuma saura 'yan mata biyu suka samu raunuka"
Kehinde Adeleke jami'in hulda da jama'a na hukumar Security and Civil Defence ya tabbatar da faruwar lamarin saidai ya bayyana cewa har yanzu ba a tabbatar da bayanan wadanda ake zargi da aikata wannan aika aika ba.
Bayan faruwar wannan lamari dai wata majiya ta bayyana cewa jami'a 'yan sanda masu aikin dakile kungiyoyin asiri, sun cafke wasu da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne madu adawa da juna, yayinda suke kokarin kaima juna hari a yankin Osogbo.
