Fadar gwamnatin ƙasar Amurka ta bayyana cewa baiwa ƙasar Ukraine damar zama ɗaya daga membobin ƙungiyar NATO a daidai wannan lokaci da suke rikici da Rasha zai jefa Amurka da ƙawayenta yaƙi da ƙasar Rasha
A wata hira da yayi da gidan talabijin na ABC News Babban mai bada shawara kan harkokin tsaro na kasar Amurka (National Security Adviser) Jake Sullivan yace " goben Ukraine na NATO babu wani maganar sasanci akan wannan batun, amma dai yayi gargaɗin cewa idan har tsohuwar tarayyar Soviet (Rasha) ta cigaba da sanya karfin soji a wannan rikici a tsakanin ta da Ukraine to hakan yana nufin Amurka zata shiga yaƙi da Rasha.
" Idan Ukraine ta shigo ƙungiyar NATO a daidai wannan lokaci da rikici ke cigaba da gudana tsakanin ta da Rasha, hakan na nufin NATO ta shiga yaƙi da Rasha, wannan kuwa na nufin tarayyar Turai ta shiga yaƙi da Rasha, amma fa daga ƙungiyar NATO har Amurka ba wanda ya shirya ma yaƙi da Rasha a yanzu" cewar Jake Sullivan.
Sullivan ya kara da cewa NATO zato karɓi Ukraine duk da rashin samun sahihiyar gayyata, amma dai dole a ɗauki wasu matakai kafin a baiwa Ukraine damar shigowa NATO a hukumance, ya kara da cewa kuma Amurka zata cigaba da baiwa Ukraine gudummawar da take bata.
Daga watan Janairu (January) zuwa yanzu Amurka da ƙawayenta sun baiwa ƙasar Ukraine alburan ƙananan makamai sama da miliyan ɗari (100 millions) da alburusan tankokin yaƙi samada dubu ɗari (100,000).
Rasaha dai na kallon wannan tarin makamai da Amurka da ƙawayenta ke jibgewa a ƙasar ta Ukraine a matsayin wani abu da zai iya canza sakamakon yaƙin nata da Ukraine, duk da cewa ƙara yawan makamai a Ukraine zai haifar da ƙarin asarar rayuka ne kawai da ƙara tsawaita yaƙin.
