Wata rundunar mai alaƙa da babbar ƙungiyar gwagwarmaya ta Hamas, da ake kira AL-AYYASH BATTALION sun fitar da wata sanarwa, inda suka tabbatar da cewa sun harba rokoki zuwa haramtattun matsugunan yahudawa dake Jenin arewacin gabar yammacin Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye.
A cikin sanarwar da suka fitar a jiya Alhamis sun bayyana cewa sun kai harin ne a Matsugunin Ram-On da roka mai suna Qassam 1.
Sun bayyana cewa wannan harin martani ne ga ta'addancin Isra'ila kan al'ummar PalasÉ—inawa gami da mamayar yahudawa ga Masallacin Quds.
Sun bayyana cewa Masallacin Quds jan layin mu ne, kuma bazamu bar sahyoniyawa suna wulakanta shi ba.
Ko a safiyar jiya Alhamis dai É—aruruwan yahudawan sahyoniya ne suka afka masallacin na Quds ta mashigar Mughrabi, ciki kuwa harda ministan tsaron Isra'ila Ben Gvir.
Sun samu rakiyar jami'an tsaron haramtacciyar ƙasar ta Isra'ila, domin su hana musulmai masu gabatar da ibada shiga Masallacin mai tsarki.
