Shugaban ƙasar Afirika ta Kudu (South Africa) Cyril Ramaphosa ya jagoranci tawagar Shugabannin kasashen Masar,Comoros, da Zambia zuwa ƙasar Ukraine.
Maƙasudin wannan ziyara dai shine tattaunawa domin shawo kan bakin zaren tsakanin ƙasar Ukraine da Rasha.
Cyril Ramaphosa ya buƙaci shugaban ƙasar ta Ukraine da ya hau teburin tattaunawa a shugaba Vladimir Putin na ƙasar Rasha, domin kawo ƙarshen yaƙin da suke gwabza wa a tsakaninsu.
Ramaphosa ya bayyana cewa a duk lokacin da aka samu saɓani a tsakanin kasashe biyu kamata yayi a nemi mafita ta hanyar tattaunawa a maimakon gwabza yaƙi, domin kuwa yaƙi yana laƙume rayukan ƴan ƙasa.
A jiya Asabar tawagar ta cilla zuwa birnin Moscow domin ganawa da shugaba Putin.
A ƴan makonin nan ne dai aka zargi ƙasar Afirika ta Kudu da baiwa ƙasar Rasha tallafin makamai domin yaƙar Ukraine, sai dai hukumomin ƙasar sun musanta hakan.
A cikin watan Agusta mai zuwa shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin zai zo taron ƙungiyar ƙasashen masu tasowa ta fannin tattalin arziƙi da zai gudana a ƙasar Afirika ta Kudu (South Africa).
