Offline

Motar Gas Tayi Bindiga A Gwagwa Da Ke Abuja.

 


A ranar alhamis ne dai aka ga wani direban motar ɗaukar gas yayi fakin cikin sauri kuma ya faɗi ma al'ummar wajen da yayi fakin cewa kowa ya gudu kafin motar tayi bindiga.


Lamarin ya auku ne a inda ake kira da mahaɗar ƴan sanda dake Gwagwa  da misalin karfe 8:30 na dare kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana ma manema labarai.


Shaidun gani da ido dai sun bayyana ma manema labarai cewa marfin ɗaya daga cikin sunduƙan gas ɗin ne ya fara ficewa hakan yasa gas ɗin dake ciki ya fara yoyo kafin daga bisani wuta ta tashi, daga karshe kuma tayi bindiga.


Mazauna Gwagwa dai sun shiga ruɗani sakamakon afkuwar wannan lamari, domin wutar ta shafe kusan awa guda tana ci.

Post a Comment

Previous Post Next Post