Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya yaba da nasarar da kungiyar Jihadin Islama ta Falasdinu ta samu a baya-bayan nan kan Isra'ila, yana mai cewa Ƙaruwar karfin kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa shi ne jigon durkusar da gwamnatin mamaya.
Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da babban sakataren kungiyar Jihad Islami ta Falasdinu Ziad al-Nakhaleh tare da tawagarsa a birnin Tehran ranar Laraba.
A ranar 9 ga watan Mayu ne gwamnatin Tel Aviv ta kaddamar da hare-haren bama-bamai a Gaza, lamarin da ya haifar da harba rokoki sama da 1,000 da kungiyar Jihad ta Islama ta yi kan Isra’ila.
Daga bisani bangarorin biyu sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a shiga tsakanin Masar bayan shafe kwanaki biyar na fafatawa, wanda yayi ajalin falasdinawa 33 a Gaza ciki har da yara shida tare da raunata 147, a cewar ma'aikatar lafiya ta Falasdinu.
Isra’ila ta kashe kwamandojin Islamic Jihadi da dama a rikicin na baya-bayan nan.
