Tsohon shugaban mayaƙan Niger Delta Dakubo Asari ya zargi gamayyar sojojin Najeriya da suka haɗa sojojin ruwa da na ƙasa da hannu wajen sace ɗanyen man ƙasarnan.
Dakubo Asari ya bayyana cewa sojojin na da hannu dumu-dumu da kaso 99 cikin 100 na satar da ake yi.
Dakubo Asari yayi wannan magana ne a lokacin wata ganawa ta musamman da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu a fadar shugaban ƙasa dake birnin tarayya Abuja.
Dakubo Asari ya bayyana ma manema labarai cewa shugaba Tinubu yayi alƙawarin yin bincike game da wannan lamari.
Ya ƙara da cewa lallai masu wannan satar suna da ƙarfi sosai dan haka dole gwamnati tayi ƙoƙari wajen daƙilesu.
Aƙarshe dai Dakubo Asari yace nan bada jimawa ba za a fara tasa ƙeyar manya masu hannu a wannan sata zuwa gidan yarin Kuje.
Rundunar sojin Najeriya dai ta musanta wannan zargi na Dakubo Asari, inda ya bayyana cewa idan da gaske yake to ya bayyana sunayen sojojin dake da hannu a satar man.
