Sabon shugaban kamfanin jiragen Najeriya Kaftin Dayo Olumide ya bayyana ma kwamitin majalisar dattawa mai kula da hidimar sufurin jiragen sama cewa jirgin da Buhari ya ƙaddamar da sunan mallakin Najeriya ne ƙarya ne, kawai yaudara ce akayi.
Ya bayyana cewa dai wannan jirgi hayar shi aka ɗauko daga Ƙasar Habasha (Ethiopia).
Ya ƙara da cewa dai tuni aka mayar da wannan jirgi inda aka karɓo hayar sa, domin dama anyi hayarsa ne na kwanaki.
Tags
Labarai
