A cigaba da zanga zangar adawa da sauya fasalin dokokin Haramtacciyar ƙasar Isra'ila, masu zanga zanga sun gudanar da zanga zanga a kusa da gidan firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu.
Anyi arangama tsakanin ƴan sanda da jami'an tsaro a wajen gidan na Netanyahu inda aka raunata wasu daga cikin masu zanga zangar aka kuma kama mutum 14 a yayin arangamar.
A wani faifan bidiyo da yayi yawo a kafafen sada zumunta anga yadda Ƴan sanda ke korar masu zanga zangar daga yankin gidan na Netanyahu inda ake ganin matakan da ƴan sanda suka ɗauka a matsayin cin zarafin ɗan adam.
Ƙungiyar masu zanga zangar mai suna "Resistance to the Dictatorship" sun yi Allah wadai da wannan aika aika ta ƴan sandan, kuma sun bayyana hakan a matsayin aikin gwamnatin kama karya.
Sun bayyana cewa dai idan aka ƙaddamar da wannan sauyin fasalin dokoki to fa zanga zanga zata zama ruwan dare a faɗin ƙasar
.jpeg)