A ranar alhamis ɗin da ta gabata ne shugaban ƙasar Amurka Joe Biden ya fadi kasa a wajen taron yaye daliban makarantar sojin sama ta ƙasar da ke garin Colorado.
Joe Biden ya fadi ne a lokacin da yake ƙoƙoarin koma kujerarsa bayan ya kammala jawabi a wajen taron shine ya zame ya faɗi ƙasa, wasu dai sunce kamar Joe biden ɗin yayi tuntuɓe ne da matakala.
A wani faifan bidiyo da yayi yawo a kafafen sada zumunta anga inda jami'an sojin saman suka yi gaggawar ɗaga Joe Biden ɗin.
Joe Biden dai yana da shekaru 80 a duniya kuma shine shugaban ƙasar Amurka mafi yawan shekaru.
Wannan dai bashi ba ne karon farko da Joe Biden ya faɗi ba, a cikin watan Nuwamban shekarar 2020 ma irin haka ta faru.
Amma fa duk da haka Joe Biden ya sake bayyana ƙudurinshi na sake tsayawa takara a zaben 2024.
Raho daga sashen labarai na FFNG Hausa.
Tags
Labarai
