Ƴan majalisar Isra'ila da aka fi sani da Knesset su shigar da wani Ƙuduri gaban majalisar ƙolin Haramtacciyar Ƙasar, ƙudurin dai zai baiwa jami'an Isra'ilar damar gudanar da tsattsauran bincike kan malamai da sauran ma'aikatan makarantun al'ummar Palasɗinu.
Daya daga cikin ƙudurorin zai baiwa kwamitin damar kora da ɗaukar ma'aikata a makarantun na Palasɗinawa.
Ƴan majalisa 45 da biyar ne suka yarda da ƙudurin inda wasu 25 suka ƙi amincewa da ƙudurin.
Tuni dai kwamitin Ma'aikatar shari'a ya rattaba hannu akan ɗaya daga cikin ƙudurorin a wannan makon.
Isra'ila dai na ɗaukar wannan mataki ne domin daƙile duk wani yunƙuri na ƙungiyar Hamas da Palestinian Islamic Jihad (PIJ)
Tags
Labarai
.jpeg)