A ranar Asabar uku ga watan Yuni da muke ciki, wani jami'in tsaron ƙasar misra (Egypt) ya kashe sojojin Isra'ila har uku a wata musayar wuta da ta auku a tsakaninsu inda daga baya shi aka kashe shi.
An dai tsinci gawar sojoji biyu na Isra'ila mace da namiji a inda suke gadi a bakin bodar da misalin karfe shida na safiyar ranar ta asabar bayan da sauran abokan aikin su suka ji shiru Radio (Walking talking) ɗinsu bata aiki, sai suka garzaya domin duba su inda suka riski gawarwakin nasu.
A sakamakon haka aka jibge sojojin Isra'ila a yankin wajen domin su gudanar da bincike sai kuma wani sabon rikici ya ɓarke inda anan wani sojan Isra'ilar ya ƙara mutuwa hakan yacika gawa ta uku, shi ma ɗan Sandan na ƙasar Misra anan ne aka kashe shi.
Mai magana da yawun rundunar sojojin ƙasar Masar Colonel Gharib Abdel-hafez ya tabbatar da cewa jami'in ɗan sandan ma'aikacin ƙasar su ne, yace lamarin kashe sojojin Isra'ila ya auku ne a lokacin da & an sandan yake bin masu sa farar kayan maye, ya bayyana hakan ne a shafin sa na Twitter.
.jpeg)