Offline

A ƙalla mutum 25 ne aka kashe a Jihar Zamfara a ranar asabar.

 


Ƙauyuka biyu ne aka kaima hari a ƙaramar hukumar mulki ta Maradun a ranar asabar ɗin da ta gabata.


Wannan hari ya biyo bayan harin da ya auku a garin Kanoma dake ƙaramar hukumar Maru a makon da ya gabata inda aka kashe mutane da dama ciki harda ƴan sa kai 16.


Ƙauyukan da aka kai harin sun haɗa da ƙauyen Jan baƙo inda aka kashe sama da mutum 20, sai kuma ƙauyen Sakkiɗa nan ma sun kashe mutum 5.


Makasan sun dira wannan ƙauyen ne da misalin karfe biyu na na dare akan babura.


Mustapha Jafaru Ƙaura mataimaki na musamman ga gwamnan jihar ta Zamfara ya bayyana cewa wannan gwamnatin bazata naɗe hannayen ta ba ana kashe al'ummar jihar ba, kuma yace suna dukkanin ƙoƙarinsu wajen tabbatar da tsaro a faɗin jihar.


Rahoto: Mahadi Tukur Almizan

Post a Comment

Previous Post Next Post