An shiga cikin ruɗani a ƙasar Afganistan a sakamakon wani mummunan harin Bom da ya auku a wani masallaci.
A ranar alhamis ne wannan harin Bom ya auku inda mutane suka taru domin gudanar da jana'izar wani shugaban Taliban mai suna Nisar Ahmad Ahmadi wanda ke rike da muƙamin gwamna a yankin.
Ahmad Ahmadi dai ya mutu ne a wani harin ƙunar ɓakin wake, inda maharin ya tada kan shi da Bom a cikin wata mota daidai lokacin da gwamnan ke wuce akan titi.
Wani mutum É—aya ya mutu wasu shida kuma sun samu rauni a wannan harin da aka kaima gwamnan.
Harin ya faru ne a masallacin Nabawi dake birnin Faizabad dake arewacin Badakshan.
A ƙalla mutum 10 goma ne suka mutu inda sama da 40 suka samu raunuka.
Tags
Labarai
