Offline

Anrasa Rayukan mutane 11 a wajen raba abincin Azumi sakamakon turmutsi-tsi a Pakistan

 



Mutane da dama kuma sun jikkata a lamarin daya auku ranar Juma'a, wanda ya faru a lokacin da daruruwan mutane suke  tura juna domin karbar abinci a wajen wata masana'anta. Wasu daga cikinsu sun fada cikin magudanar ruwa da ke kusa, in ji jami’in ‘yan sanda Mughees Hashmi.


Mazauna yankin sun ce wata katanga ta kuma ruguje kusa da magudanar ruwa, lamarin da ya yi sanadin raunata tare da kashe mutane yayin turmutsitsin.


Kafofin yada labaran cikin gida sun ruwaito cewa mata takwas da yara uku sun mutu.


Hashmi ya ce mamallakin masana’antar da ya shirya cibiyar rarraba abinci bai sanar da ‘yan sanda game da shirin ba. Ya ce ‘yan sandan yankin ba su da masaniyar rabon kayayyakin, idan ba haka ba za su iya tura sojoji.


Ministan harkokin wajen kasar Bilawal Bhutto Zardari wanda ya fito daga lardin Sindh, babban birnin kasar Karachi, ya umarci hukumomi da su binciki abin da ya haddasa lamarin.


Wannan dai dai shi ne mafi muni a wuraren rabon abinci na watan Ramadan tun bayan da aka fara azumin watan azumi a makon jiya.


A wani lamari na baya-bayan nan, adadin wadanda suka mutu sakamakon turmutsutsu a cibiyoyin raba abinci kyauta a fadin kasar ya karu zuwa akalla 21 tun daga makon jiya.


Wani mazaunin yankin, Mohammad Arsalan ya ce yana zaune ne a kusa da masana’antar da jama’a suka taru tun da safe domin karbar abincin kyauta. Ya ce bai san hakikanin abin da ya haddasa lamarin ba, amma “mun ji kuka kuma daga baya muka samu labarin wannan turmutsutsu”.


Lamarin na ranar Juma’a ya zo ne kwana guda bayan da hukumomi suka ba da umarnin tura karin ‘yan sanda a cibiyoyin rarraba abinci na Ramadan domin kaucewa cunkoso mai hatsari.


Pakistan mai karancin kudi tana fuskantar daya daga cikin mafi munin rikicin tattalin arziki a tarihinta. Miliyoyin mutane ne ke kokawa wajen sanya abinci a kan teburi yayin da matsalar tsadar rayuwa ke kara ta'azzara.


Jama'a da dama ne suke taruwa a wuraren rabon abinci tun bayan da gwamnati ta kaddamar da wani shiri a makon da ya gabata na bayar da fulawa kyauta ga iyalai masu karamin karfi a cikin watan azumin Ramadan domin rage tasirin hauhawar farashin kayayyaki da kuma talauci.


Kokarin ci gaba da bunkasar tattalin arzikin kasar, gwamnati ta yi fatan cimma yarjejeniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) don dawo da shirin lamuni na dala biliyan 6.5 da aka dakatar tun watan Nuwamba.


IMF ta gabatar da wasu bukatu na sakin wani kaso na $1.1bn. Ya haɗa da sassaucin ra'ayi na musayar kuɗin rupee, cire tallafi da haɓaka haraji.


A ranar Juma'ar da ta gabata, firaministan Pakistan Shahbaz Sharif ya ziyarci wata cibiyar rarraba fulawa da ke Islamabad, babban birnin kasar, inda ya gana da mata da suka zo karbar garin fulawar. Sharif ya roki hukumomi da su tabbatar da cewa an kyautata wa mutane kuma ba a sake samun wata matsala ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post