Offline

Iran ta gargadi Azerbaijan game da "Isra'ila".

 


Da yake sukar Jamhuriyar Azarbaijan saboda ƙin bayar da bayani game da haɓaka haɗin gwiwa da gwamnatin sahyoniyawan da kuma yin sabbin zarge-zarge a kan Iran, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran ya gargaɗi Baku game da munanan manufofin gwamnatin "Isra'ila".


A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a daren jiya Juma'a, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasser Kanaani ya ce kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Azarbaijan ya sake yin sabbin zarge-zarge kan kasar Iran tare da kaucewa wani bayani kan kalaman da ministan harkokin wajen gwamnatin sahyoniyawan ya yi kan Iran din. yarjejeniya tare da takwaransa na Azerbaijan  "haÉ—in kai domin adawa da Iran".


"Shin ci gaba da yin shirun Azerbaijan ba wani bu bane da yake tabbatar wancan haÉ—in gwuiwar na adawa da Iran ba?


Daga nan sai ya gargadi jami'an Azerbaijan cewa manufar daya tilo da ke tattare da yunkurin gwamnatin sahyoniya mai muggan laifuka akan kasashen musulmi ita ce "kirkirar sabani da rarrabuwar kawuna a cikin al'ummar musulmi domin cimma manufofinta".


Kakakin na Iran ya ce "Muna shawartar 'yan'uwanmu musulmi a Azarbaijan  da su yi taka tsantsan game da hakikanin makiya wato sahyoniyawa.


A wani jawabi da ya yi da ministan harkokin wajen Azerbaijan Jeyhun Bayramov a birnin al-Quds (Jerusalem) da Isra'ila ta mamaye a ranar Laraba, ministan harkokin wajen Isra'ila Eli Cohen ya yaba da bude ofishin jakadancin Azerbaijan a Tel Aviv a matsayin wata shaida ta "karfafa dangantaka. ” tsakanin bangarorin biyu.


Cohen ya kuma yi iƙirarin cewa shi da ministan harkokin wajen Azerbaijan sun amince da "haɗa kai akan Iran tare da ƙarfafa haɗin gwiwar kasashen biyu a fannonin tattalin arziki, tsaro, makamashi da kere-kere."


A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar 29 ga watan Maris, Bayramov ya ce ya yi matukar farin cikin tarbe shi da firaministan gwamnatin sahyoniyawan yayi a ziyarar aiki da ya kai kasar ta "Isra'ila".


Ministan harkokin wajen kasar Azerbaijan ya kuma yaba da bude ofishin jakadancin kasarsa a Tel Aviv a matsayin wani sabon mataki na kawance da gwamnatin sahyoniya.


A ranar Juma'a Kanaani ya gargadi gwamnatin kasar Azarbaijan da ta kaucewa tarkon da makiyan alakar da ke tsakaninta da Iran suka kulla.


Haka nan kuma ya kara da cewa, a dabi'ance Iran ba za ta ci gaba da nuna halin ko-in-kula da makirce-makircen da yahudawan sahyoniya suke yi wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran da aka kitsa daga Jamhuriyar Azarbaijan ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post