Offline

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran: Iran ta yi bikin cika shekaru 44 da kawo Ƙarshen Mulkin Pahlavi da Amurka ke marawa baya

 



Kasar Iran na gudanar da bukukuwan cika shekaru 44 da kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a bayan zaben raba gardama mai cike da tarihi, inda al'ummar Iran suka kada kuri'ar amincewa da ficewa daga mulkin, makwanni bayan rugujewar gwamnatin Pahlavi da Amurka ke marawa baya.


A wani gagarumin zaben raba gardama na kwanaki biyu da aka gudanar a tsakanin ranakun 30-31 ga Maris, 1979, fiye da kashi 98.2 cikin 100 na Iraniyawan da suka cancanta suka kada kuri'ar "eh" don kafa Jamhuriyar Musulunci a kasar.


Zaben wanda aka gudanar kasa da watanni biyu bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, ana daukarsa a matsayin wani sauyi a tarihin Iran.


An kafa jamhuriyar Musulunci a Iran ne mai taken juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979 wanda ya yi kira ga  "Yanci, da Jamhuriyar Musulunci".


Tun daga wannan lokacin ne al'ummar kasar ke bikin ranar 12 ga watan Farvardin a kowace shekara a kalandar Iran a matsayin ranar Jamhuriyar Musulunci.


Juyin juya halin Musulunci karkashin jagorancin marigayi Imam Khumaini ya kawo  kifar da gwamnatin Mohammad Reza Pahlavi tare da kawo karshen mulkin sarauta na tsawon shekaru 2,500 a Iran.

Post a Comment

Previous Post Next Post