Offline

Wanene Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) !


 

Daga Idishia Jos 


Takaitaccen tarihin rayuwar jagoran harkar musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Zakzaky.


Rana Da Wajen Da Aka Haifi Sheikh:

An haifi Sheikh ne a ranar 5 ga watan Mayu shekara ta 1953 (15 ga Sha'aban 1372 AH) a garin Zaria dake cikin jihar Kaduna a Tarayyar Nigeria, kuma sunan sa Zakzaky kalma ce dake nufin 'mutumin zazzau'.


Sheikh Ibraheem Zakzaky shine ɗan Yaqoub shi kuma dan Aliyu shi kuwa dan Tajuddin dan Imam Hussain. Shi Imam Hussain wani bawan Allah ne daya fito daga Mali yazo garin Sokoto a lokacin Mujaddadi Sheikh Usman dan Fodiyo (RA) ya zauna tare da shi a matsayin almajirin sa, ta haka nema a lokacin da Shehu Usman dan Fodio (RA) ya naɗa Mallam Musa a matsayin Amir na lardin zazzau sai ya hada shi da Imam Hussain a matsayin mai bashi shawara. Ta haka ne a hankali-a hankali auratayya ta rika shiga tsakanin iyalen su kuma suka zama 'Ƴan'uwan juna ta wannan tun a farkon ƙarni na 19.


Mahaifin Sheikh Ibrahim Zakzaky mai suna Yaƙoub, ya rasu ne tun shekara ta 1972, daga bisani kuma mahaifiyar sa ta rasu a shekarar 25 ga watan Muharram 1436 wato 2014, kuma Sheikh Ibraheem Zakzaky shine na biyar a wajen mahaifin su.


Mata Da Yara:

Sheikh yana da mace daya Malama Zeenatudden da kuma yaya tara, guda 7 maza sune, Muhammad, Ahmad, Hameed, Mahmoud, Aliyu, Hammad, Da Humaid. Mata kuma su 2 ne Suhaila da Nusaiba. 


Karatun Sa:

Sheikh Ibrahim Zakzaky ya fara karatu ne tun yana yaro karami a makarantar koyon karatun Al-kurani mai girma a makarantun Allo na al'ada kamar yadda aka saba tare da surkawa da karatun ilmin addinin musulunci wajen manyan malamai na wancan lokacin har ya zuwa lokacin da ya kai shekaru goma sha shida inda ya fara haduwa da tsarin karatu na zamani a shekara ta 1979 inda ya fara karatu a makarantar horar da malaman Arabiyya dake Zaria. 


Sannan daga shekara ta 1971-1975 ya shiga makarantar koyon larabci ta Kano watau School for Arabic Studies (SAS) wadda aka gina tun 1934 a matsayin makarantar koyon aikin lauya. sannan kuma daga baya ita ce ta haifar da babbar jami'ar Bayero da aka sani a yanzu. 


Saboda irin yadda Sheikh Zakzaky yake da ra'ayin faÉ—aÉ—a ilmin sa kan wasu darussa da ba'a koyarwa a wannan makaranta yasa ya gwama karatun nasa na Grade II da wasu maddoji ba tare da yayi su a baya ba kamar sanin gwamnati (Government) da ilmin tattalin arziki (Economics) inda yayi jarabawar GCE a kansu.


Daga bisani Sheikh yayi jarabawa ta gaba (Advanced level GCE) akan waÉ—annan maddojin:Government, Economics, Hausa, da kuma Islamic Studies inda ya sami kyakyawan natija wadda ta bashi damar shiga jami'a kai tsaye a shekara ta 1976 zuwa 1979 inda ya fara karatun digirin farko (B. Sc) akan sanin tattalin arziki (Economics).


Sheikh yayi musharaka cikin kungiyar dalibai ta musulmi inda ya zama fitaccen mamba a cikin makaranta da kuma matsayin ƙasa baki ɗaya inda a shekara ta 1978 ya zama babban sakataren kungiyar na kasa sannan kuma yayi zama mataimakin shugaban kungiyar bangaren harkokin kasashen waje a shekara ta 1979. Sheikh Zakzaky yana daya daga cikin wadanda suka jagoranci kare Shari'ah a lokacin da aka yi wani jerin gwano na nuna goyon baya ga Shari'ah a baƙi dayan kasar.


Ayyukan Sa:

Babban aikin da Sheikh Ibrahim Zakzaky ya sanya a gaba shine karatu da kuma yada ilmi, yana gabatar da jawabansa yawanci da Hausa sai kuma Turanci. Dr. Iqbal Siddiqui ya taba siffanta Sheikh a matsayin "Kashin bayan harkar musulunci a Nigeria" Babban manufar harkar musulunci da Sheikh yakewa jagoranci shine wayar da kan musulmi abin daya doru a kansu a matsayin su na É—aiÉ—aiku da kuma al'umma.


Yanzun haka harkar musulunci tana da makarantu dake karkashin ta na Primary da kuma gaba da Primary, makarantu an yi musu suna da makarantun Fudiyya. Haka kuma akwai cibiyoyi da da wuraren bincike da dama a manyan garuruwa na kasar karkashin wannan harka. Harkar ta mallaki jaridar da tafi ko wacce a kasar shiga ko ina da harsheen Hausa wadda ake kira Al-mizan. 


Sheikh ya sami matsala da hukumomi cikin kaki ko fararen kaya wadanda suke ganin cewa irin salon wa'azin nasa yana barazana ga mulkin su. A lokacin General Sani Abacha an kama Sheikh ne da tuhumar yana wa'azin 'babu hukuma sai ta Allah'.


A halin da ake ciki dai yanzun haka harkar musulunci karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky ta cika shekaru 40 tana kira kan komowa karkashin tsari na musulunci.


Kyautansa:

Sheikh Zakzaky an shaideshi da yawan kyauta, akwai Lokacin da ya sayawa makafin garin Zariya gida ya basu, sannan duk shekara a Anguwar sa Gyellesu yana raba kayayyakin abinci da na masarufi, har bayan WaÆ™iyar Zariya Sheikh Zakzaky duk shekara sai ya aiko da kayayyakin abinci yadda ya saba. Musamman a shekara ta 13-ga watan Mayu-2020 Sheikh Zakzaky ya raba kayayyakin abinci ga mabuÆ™ata sama da 111,000 a faÉ—in Æ™asar Nigeriya. 


Tsawon Tsarewar Da Aka Yiwa Sheikh:

Sheikh Ibrahim Zakzaky ya kwashe shekaru tara a tsare a kurkuku daban-daban na kasar, daga shekara ta 1981-1984 an É—aure shi a kurkukun Enugu sai kuma kurkukun neman bayanai da bincike na jami'an leken asiri na kasa dake Lagos (Intorregation center) a shekara ta 1984-1985 sai kuma Kiri-kiri a shekara ta 1985 kurkukun Port harcout daga 1987-1989 sannan daga 1996-1997 duk dai a can Port Harcout. Sai kuma kurkukun Kaduna a 1987 sannan daga 1997-1998. Sai kuma haramtacciyar tsarewar da gwamnatin Buhari taylke yi masa yanzu tun 2015-2021 É—in shekarar nan. 


Wakiyoyi:

An yi wakiyoyi dadan gaske a wannan harka kamar wakiyar, Abacha, wakiyar Ƙofar Doka, WaÆ™iyar Kaduna Poly, WaÆ™iyar Laraba Kaduna, WaÆ™iyar kama Malama Zeenat, WaÆ™iyar Qudus 1999, Kona gidan Alhaji ÆŠanlami, WaÆ™iyar Alu Wammako 2017, WaÆ™iyar Qudus Zariya 2009, Arba'een Abuja, WaÆ™iyar Ashura Funtuwa, Kaduna, Kano da Jos. 


Sannan kuma WaÆ™iyar Zariya 2015 wanda ita ce ta danne dukkan wakiyoyin nan da aka gabata. Saboda itace aka kashe Almajiran Sheikh Zakzaky sama da mutane 1000+, aka rusa muhallan Harka islamiyya baki daya dake garin Zariya. Daga ciki akwai, Gidan Sheikh Zakzaky (H) dake Gyellesu, Hussainiyya Bakiyatullah, Darur Rahma maÆ™abatar shahidai, Fudiyya Islamic Center, Fudiyya Secondary School, da kuma gidan makwancin mahaifiyar Sheikh Zakzaky (H) Malama Suhaila. 


Tsarewar Gwamnatin Buhari:

Gwamnatin Buhari tana tsare da Sheikh Zakzaky (H) tun shekarar 2015 shekaru 5 kenan, bayan kisan kiyashin Zariya wanda sojoji Nigeriya suka yi a ranar 15-December-2015. Daga bisani kuma kotun tarayya dake Abuja ta yanke shari'ar sakin Sheikh Zakzaky amma gwamnatin taki bin wannan umarnin. A shekarar 2018 ne kuma aka mayar Sheikh Zakzaky gidan yarin garin Kaduna inda ake cigaba da haramtacciyar tsare shi. 


A shekara 2023 É—in nan wanda yayi daidai da 1444Ah Sheikh Ibraheem Zakzaky ya cika shekaru 72 a duniya,  baya ga shafe shekaru 5 ana gudanar da bikin Nisfu Sha'aban yana hannun gwamnati Nigeriya biyo bayan kisan kiyashin Zariya ta wakiyar Buhari. 


Daga Idris Umar Abdullahi.

-Idishia Jos

idrisu250@gmail.com

08036204874

Post a Comment

Previous Post Next Post