–Muh'd M. Ndanusa
Wannan sakon taya murnar haihuwa na musamman ne ba kamar saura ba, rubutun jinjina ne ga mutumin kiriki, wanda ya shiga gaba domin haska wa mutane hanya da take da tsananin duhu da hadarin gaske, sauran mutane kuwa na biye.
Halin da Najeriya ke ciki yanzu, ya yi kama da irin shirin fim din ban-tsoro, wanda mutane ke zama mashaya jinin junansu bil-adama, inda ran mutum ke zama ba a bakin komai ba daga hannun mashaya jinin da sun zaku su ga jinin wa za su sha a gaba.
A dai-dai irin wannan lokacin, a wannan kasar da malaman addini, sarakunan gargajiya, da 'yan siyasa su ka zama yan kasuwar da ke sayar da mabiyansu domin abin duniya, abin godiya ne samun mutum da yai daban irin Sheikh Zakzaky.
Samun shugaba wanda al'umma da ci gabanta ya dame sa, ba wai wadanda su kawai aljihunsu da abinda za su samu ne gabansu ba, abin jin dadi ne.
Shi din mutum ne wanda ke aikata kalamansa, ba sabanin sa ba wanda sam ba ya aikata abinda ya ke fada ba.
Sheikh Zakzaky ya tabbatar da cewa hanyar da yake kira a kai ita ce kadai mafita ga matsalolin Najeriya. A fili yake wannan za a iya fahimta. Ta doru ne a kan gaskiya da adalci. Babban burin Harkar Musulunci shi ne samar da al'umma bisa turba ta gaskiya, da tabbatar da adalci ga kowa ba tare da la'akari da banbancin yare, jinsi ko addini ba.
Kar ka dogara da surutun masu suka, dan yi bincike da kan ka, ka nemi sanin sa da gwagwarmayarsa ta ingantattun hanyoyi. Duk yunkurin sa na samun kyakkyawar kasa ne.
Ma su suka sun yi ta yada karairayi dangane da Sheikh Zakzaky, amma duk da haka, duniya ta shaide shi da shi mutum ne mai hakuri da son zaman lafiya. Shi ne wanda ya ba Kiristoci kariya a gidansa da ke Zariya.
Da a ce Sheikh Zakzaky mai son rikici ne ba zaman lafiya ba, da yanzu ba wata kasa wai ita Najeriya. Shi ke da mabiyan da a shirye su ke kuma za su iya tsayar da komai a kasar, amman duk da haka ya yi kira da a zauna lafiya a lokacin da sojoji su ka kashe masa hazikan 'yaya uku ranar 25 ga Yulin 2014.
A Disambar 2015, sojoji sun sake kai masa hari a gidansa da ke Zariya, inda su ka kara kashe wasu 'yayansa uku. Shi da matarsa kuwa an masu manyan raunuka masu hadari. An kuma kashe mabiyansa fiye da 1,000.
Babu, na kara maimaitawa, babu wani shugaba da zai yi hakuri ya kauda kai bayan fuskantar irin wannan zaluncin. Duk da wannan, Sheikh Zakzaky na a natse, ya tsayu kyam, kuma bai tada rikici ba.
Yau ka ke cika shekara 72, tabbas duniya na alfahari da kai, kuma tarihi ba zai taba mantawa da tsayuwarka, sadaukarwa da jajircewa ba.
Na yi aiki a matakai daban-daban, kama daga aikin gwamnati, fannin masana kwararru, aikin kanfanoni da masana'antu, na yi hulda da shuwagabanni da kuma masu fada a ji na kasa, amman ban taba ganin mutum kamili, mai gaskiya da amana, wanda yake kamili kuma tsayayyen shugaba kamar ka ba.
Barka da ranar haihuwa, ya uban raunana. Allah Ya dade ka da tsawon rai da lafiya tare da cikar burinka na ganin gyaruwar Najeriya.
