Daga Saifullahi M. Kabir
Yau Talata, 15 ga watan Sha’aban 1444, Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke cika shekaru 72 da haihuwa.
An haifi Shaikh Ibraheem Zakzaky ne a ranar Talata 15 ga Sha’aban, a shekarar 1372 Hijiriyya, ya dace da 28 ga watan Afrilu 1953, a unguwar Kwarbai da ke cikin garin Zariya ta jihar Kaduna.
Mahaifinsa shine Malam Yaqoub dan Malam Ali dan Sharif Tajuddeen dan Limam Husaini. Liman Husaini, a wancan lokacin shine babban limamin wani gari da ake ce ma Shingixi, da ke tsohuwar Daular Mali ta da, kuma asalinsu Idrisiyyawa ne, wato Sharifan da suke da dangane da Imam Hasanul Mujtaba (AS) ta tsatson jikansa Muhammad Nafsuz-Zakiyya, ta hanyar Idris dan Idris.
Tarihi ya nuna cewa a lokacin jihadin Shehu Usman Danfodiye, kimanin shekaru 220 da suka gabata, Liman Husaini na daya daga cikin mutanen da suka taho daga Daular Mali, da nufin su taimaki Shehu a yunkurin tabbatar da addinin Musulunci da yake yi. Daga baya, Liman Husaini ya kasance tare da Malam Musa a yayin da Shehu ya turo shi da tutar jihadi a matsayin wakilinsa a lardin Zazzau.
Bayan isowarsu Zariya, har zuwa rasuwar Malam Musa, sannan sai Liman Husaini ya bar Zariya ya koma Mali, inda bayan wasu shekaru a yayin da mulkin Zazzau ya koma hannun dan Malam Musa mai suna Abdulkadir (Sidi) a wajajen shekarar 1850 Miladiyya –kimanin shekaru 170 da suka gabata, sai dan Liman Husaini, mai suna Sharif Tajudden ya sake dawowa Zariya tare da wasu ‘yan uwansa Sharifai.
Bayan zuwan Sharif Tajudden, an yi musu masauki ne a Kwarbai, amma daga baya bisa zabin kansa ya koma Likoro, inda ya kafa babban makarantar Alkur’ani da koyar da littafai a nan, kuma Allah ya kaddara ya haifi ‘ya’ya biyar da matarsa A’isha, na karshe a cikin ‘ya’yan nashi shine Malam Ali, kakan Shaikh Zakzaky na farko.
Bayan tasowar Malam Ali, ya fara karatu a wajen mahaifinsa, daga baya Sarkin Zazzau Ali Dan Sidi ya ba da shawara aka tura shi Gabas (Borno) don ya je ya haddace Alkur’ani. Ance Malam Ali bai dawo gida ba sai da ya samu labarin rasuwar mahaifinsa, bayan ya haddace Alkur’ani har ya tara dalibai, don haka da ya dawo sai Sarkin Zazzau Ali ya nemi ya tsaya a Zariya, ya gina masa makaranta a bayan fadar Zazzau inda ya cigaba da karantarwa.
Malam Ali ya auri wata mai suna Hajara, wacce ake kiranta da suna Mai Karatu saboda tsabar iliminta, sai Allah ya kaddara musu samun ‘ya’ya hudu, mata uku a jere sannan aka samu namiji wanda aka saka masa suna Yaqoub. Malam Yaqoub shine mahaifin Shaikh Ibraheem Zakzaky.
Kamar sauran iyayensa, shima Malam Yaqoub ya taso ne da karatun Alkur’ani da na littafan addini, sai dai shi an ce bai tara dalibai da yawa ba, ‘yan gidansu kawai ya karantar Alkur’ani. Kuma ya auri mata biyu, daga cikinsu akwai Malama Saliha, wacce aka fi sani da Malama Hari Jamo, ta haifa masa ‘ya’ya kimanin 11, Shaikh Ibraheem Zakzaky shine na biyar a cikin ‘ya’yanta.
Shaikh Zakzaky ya taso da karatun littafan addini a zaurukan Malamai, inda baya ga karatu a wajen mahaifinsa Malam Yaqoub da kakarsa Malama Maikaratu da kuma mahaifiyarsa Malama Saliha, ya kuma yi makarantar Malam Sani Abdulkadir, da ta Malam Sani Na’ibin Zazzau, da ta Malam Isa na Madaka, da wajen Malam Ibrahim na Kakaki, duk a Zariya.
Sannan kuma a Kano Shaikh Zakzaky ya yi karatu a zaurukan Malam Nuhu limamin Yola, wanda (Yola din) wata unguwa ce a cikin birnin Kano, sannan ya yi karatu a wajen Malam Isa Waziri, da wajen Malam Shawish Abdallah (Baqadire), da sauransu.
Bincike ya tabbatar da cewa Shaikh Zakzaky ya karanta fannoni daban-daban na Luga, Nahawu da Sarfu, Fiqihu da Tafsirin Alkur’ani da sauransu. Tun bai fi shekaru 20 da haihuwa ba ya karance littafan da ake karanta su a zaurukan ilimi irinsu Ajuruma, Mulha, Saja’i, Alfiyan Danmaliki, da wasu littafan da suka shafi Luggan Larabci kamar Ishiriniya, Witiriya, Ashariya har ma da Makamatul Hariri da Shu’ara’ul Jahiliyya. Haka ma a bangaren Fiqihun Malikiyya, Shaikh ya kai ma sauke har Muktasar a wannan lokacin.
A shekarar 1969, lokacin yana dan shekaru 16 da haihuwa, wato bayan ya sauke Alkur’ani, a lokaci guda yana yin karatun littafai a zauruka, sai kuma aka saka shi a makarantar Nizamiyya, inda ya fara da wata makaranta ta koyon Larabci a garin Zariya, wacce ake kiranta Zaria Provincial School. Shaikh Zakzaky ya yi karatu a makarantar ne na tsawon shekaru biyu. Wato daga shekarar 1969 zuwa 1971 ya kammala ta.
Bayan kammala karatun Shaikh Zakzaky a makarantar Zaria Provincial Arabic School, a tsakiyar shekarar 1971 ya tafi wata makaranta da ake ce mata Madarasatul Ulumul Arabiyya (School for Arabic Studies -SAS) a garin Kano, inda ya shafe shekaru hudu yana karatu a cikinta (1971 zuwa 1975).
A wannan makaranta ta SAS, Kano, ana tarbiyar Malamai ne don su je su koyar a mataki mafi inganci a makarantu a bangaren Larabci da addini. Don haka an fi karfafa karatun addini a cikinsa. Amma sai ya kasance akwai wasu darussan ‘Advance Level’, da mutum yake da zabi ya jona su da karatunsa, sai ya rika zuwa ana musu ‘lesson’ dinsu da yamma (wato ba a ainihin lokacin makarantar ba). Kuma mutum na iya zana jarabawar shiga Jami’a daga wannan Advance level din.
Shaikh Zakzaky a wannan lokacin, bisa zabin kansa ya jona wannan ‘Advance level’ din, inda ya karanta English literature, Economics, Government, Hausa, Arabiyya da kuma Islamic studies.
Bayan kammalata a shekarar 1975, sai ya zana jarabawar gama makarantar SAS din (Grade II Certificate), sannan kuma ya zana jarabawar wadannan darussan da ya yi a ‘Advance Level’ din. Sai ya zama ya zana jarabawa kashi biyu, kuma duk biyun suka fito a kusan lokaci guda duk ya ci su. Wato ya ci jarabawarsa ta Grade 2, ya kuma ci Jarabawar da ya yi na wasu fannoni guda hudu, wato Economics, Hausa, Government da kuma Islamic Studies.
Fitowar wannan jarabawar ta ‘Advance level’ a shekarar 1976 kuma ya zama ya ci, wannan ya bashi damar fara karatun Jami’ar Ahmadu Bello, kai tsaye ba tare da sharan fage ba.
Shigan Shaikh Zakzaky jami’ar ABU ke da wuya ya fara harkokin addinin Musulunci a karkashin kungiyar Dalibai Musulmi ta MSSN, wanda ya rika amfani da damar wajen fadakar da al’umma manufar halittarsu da kuma aikin da ya dace su tsayu da su don neman uzuri a wajen Allah Ta’ala, inda a karshe Shaikh Zakzaky bayan shafe shekaru kamar uku yana kiran mutane zuwa ga addini tare da kwakkwafe tunaninsu a sirrance, a shekarar 1980 ya shelanta da’awar a bainal-jama’a a garin Funtua.
Daga nan Da’awar Shaikh Zakzaky ta fara karbuwa har ga mutanen gari, inda su kuma hukumomin kasa suka saka masa ido da kokarin kawar da shi da kawo karshen kiran da yake yi tun a farkon al’amarin.
A shekarar 1981 ne shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari ya kama Shaikh Zakzaky ya tsare har sai a shekarar 1984 bayan Buhari ya hambare gwamnatin Shagari sannan aka saki Shaikh din.
Shima kuma Buharin ya kama Shaikh Zakzaky a shekarar 1984, sai da Babangida ya hambare gwamnatin Buhari sannan aka saki Shaikh din a shekarar 1985. Sannan kuma shima Janar Babangida ya kama Shaikh din a shekarar 1987 zuwa 1989 sannan aka sake shi.
A shekarar 1996 ma Janaral Sani Abacha ya kama Shaikh Zakzaky, inda sai bayan da Abachan ya mutu, a karshen shekarar 1998 Allah ya kaddara kubutan Shaikh Zakzaky daga kurkukun Abacha.
Sannan kuma Muhammadu Buhari ya kuma kama Shaikh din ya tsare a kurkuku tsawon shekaru shida, tun daga Disambar 2015 har zuwa watan Yulin 2021 sannan aka sake shi. Ya kama shi ne bayan da ya yi yunkurin kashe shi ta hanyar aika sojoji, wadanda suka bude wuta a gidanshi suka kashe mutane fiye da dubu, sannan suka harbe shi da mai dakinsa, suka kuma kama su aka tsare su tare tsawon wadannan shekarun.
Shaikh Zakzaky ya yi karatun addini bangaren Jafariyya a wajen Malamai daban-daban, daga cikinsu akwai Sayyid Tabataba’i a tsakanin shekarar 1990 zuwa 1993 a Ghana, sannan kuma a shekarar 2000 zuwa shekarar 2015 ya rika zuwa Jamhuriyyar Musulunci ta Iran yana karatun littafan Imamiyyah da Lugan Larabci a wajen Malamai daban-daban, daga ciki akwai Shaikh Jafarul Hadi, da Shaikh Dabasi da Ayatullah Ahmadi, Sayyid Ridawi da Farfesa Dahiri da sauransu
Shaikh Ibraheem Zakzaky, wanda yake da miliyoyin mabiya da magoya da suka amsa da’awarsa, ya je kasashe da dama don halartar tarurrukan addini. Ya kuma yi aikin Hajji sau takwas a rayuwarsa, ya rika zuwa Umara inda yake kwashe baki dayan watan Ramadan a Makkah shima sau takwas din. Ya kuma ziyarci haramomin Ma’asumai (AS) baki daya a Iraqi da Iran da Madina a lokuta daban-daban.
Shaikh Zakzaky ya rika karantar da fannoni daban-daban na ilimin addini, musamman Tafsirin Alkur’ani da kuma Sharhin Nahjul Balagha da yake gabatarwa ga mutane tsawon shekaru a matakin ‘Aama’, da kuma wasu fannonin ilimi da suka hada da Fiqihu, Akhlaq da sauransu da ya rika karantar da wasu daga manyan almajiransa a matakin ‘Khas’.
Da’awar Shaikh Zakzaky ta samu goyon baya daga wajen Malaman Musulunci da dama daga bangarorin Shi’a da Sunnah, haka ma manyan masana, kai har da wadanda ma ba Musulmi ba.
A ranar 29/12/2015, yayin ganawarsa da mahalarta taron hadin kan Musulmi, Jagoran Juyin Musulunci na Iran, kuma Babban Malamin Musulmin Duniya, Marja’i, Ayatullahi Sayyid Ali Khamene’i ke ma Shaikh Zakzaky kirari da: “Masani, ‘Muslihi’, mai kawo gyara da kokarin hadin kan musulmi, kuma mumini.”
Haka kuma da yake ganawa da masana adabi da mawaka na kasar Iran a ranar Litini 20/06/2016, Ayatullah Sayyid Ali Khamene’i ya siffanta Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da Mujahidi, Jarumi kuma tsayayyen Malami na Nijeriya.
Shima Shugaban Mabiya Mazhabar Ahlulbait (AS) a kasar Ghana, Shaikh Abubakar Ahmad Jamaluddeen a jawabinsa na rufe Tattakin Arba’een din 2017 a birnin Accra, ya bayyana Shaikh Zakzaky a matsayin daya daga cikin Malaman Shi’a a duniya. Inda yace: “Shaikh Zakzaky kamar sauran malaman Shi’a na duniya, ana gallaza masa bisa zalunci. Idan za ka tambayi duniya, menene laifin da Shaikh Zakzaky ya yi? Za a ce maka babu wani laifi da ya taba aikatawa!”
Farfesa Hassan Shuja’i Fard, wakilin Shaikh Zakzaky a kan harkokin da suka shafi kasashen waje, a wajen taron baje kolin Alkur’ani wanda ya gudana ranar 16/5/2019 a birnin Tehran, Iran, ya ambata cewa: “Lamarin Shaikh Zakzaky da da’awarsa abu ne da tun ran gini ran zane. Na taba karanta busharar bayyanar Shaikh Zakzaky da fara da’awarsa. Tun kimanin fiye da shekaru 200 da suka gabata, Shehu Usman bin Fodiye ya yi busharar bayyanar wani mai kira, kuma ya fadi suna, siffofi da lokacin da zai bayyana, kuma a daidai lokacin da aka ambata ne Shaikh Zakzaky ya bayyana”.
A jawabinsa na Ranar Maulidin Manzon Allah (S) a birnin Lebanon, ranar 29/12/2015, Shugaban Kungiyar Hizbullah, Sayyid Hassan Nasrullah, ya yaba da irin juriya da hakuri irin na Shaikh Zakzaky. Yace: “Irin wannan wayewa da shugabanci na gaskiya (daga Shaikh Zakzaky), duk da irin matsayinsa, amma halin dattakunsa ya kawo karshen wannan al’amari da ka iya kawo hatsaniya, wannan hali, hali ne na koyi, kuma abin alfahari ga kasa, kuma ya cancanci goyon baya da girmamawa!”
A lokacin ganawarsa da Iyalan Sayyid Zakzaky, a Birnin Qum na Iran. ranar Litinin 30/12/2019, shugaban mabiya Mazhabar Ahlulbait a Bahrain, Shaikh Issa Qaseem, ya bayyana cewa: “Shaikh Zakzaky, yana samun matsayi mai girma a zukatan Muminai, hakika Allah ya daukaka ambatonsa a Duniya, kuma zai daukaka shi a Lahira Insha Allah.”
Yace: “Sheikh Zakzaky ya wayi gari a matsayin wata Makaranta a cikin Najeriya da wajenta, ta bangaren kokari da sadaukarwarsa, (Sheikh Zakzaky) Makaranta ne shi, wadda take koyar da mu yadda ake yin Jihadi a Tafarkin Allah, tana koyar da mu sallamawa da sadaukarwa a hanyar Allah, da kuma yin aiki domin neman yardar Allah madaukakin Sarki.”
Ta bangaren wadanda ba Musulmi ba kuwa, akwai wani Pasto Methosela Ndoma wanda ke da babban Coci a Abuja, a yayin da almajiran Shaikh Zakzaky suka je masa gaisuwar Kirsimeti don karfafa hadin kai a ranar Talata 20/12/2016. Ya bayyana cewa: “Shaikh Zakzaky mutum ne da babu kamarsa a fadin kasar nan, shi ne asalin mai yaki da cin hanci da rashawa. Ba duniya ce a gabansa ba, shiriyar al’umma ita ce babban burinsa!”
Ya kara da cewa: “Ba na tunanin shiga mawuyacin hali kowane iri ne indai akan Shaikh Zakzaky ne. Na mammanna hotunansa a falona, saboda duk wanda ya shigo ya gane ni almajirinsa ne. An kori matata a aiki saboda muna tare da ‘yan Shi’a ne (almajiran Shakh Zakzaky), amma duk wannan bai dame ni ba!”
Shima shugaban Cocin Jama’are ta jihar Bauchi, Rebaran Philips a yayin da Dandalin Daliban Harkar Musulunci suka ziyarci cocinsa, a ranar ranar Lahadi 12/1/2020, ya bayyana cewa: “Kullum ana cewa Musulunci addinin zaman lafiya ne, Kalmar ‘ISLAM’ tana nufin zaman lafiya, amma ban taba yarda ba, sai a wurin Shaikh Zakzaky! Da a ce a kasar nan za a samu ire-iren Shaikh Zakzaky, da Nijeriya ta zauna cikin Salama! El-Zakzaky ‘Super Human Being’ ne!”
Hajiya Naja’atu Muhammed, fitacciyar ‘yar siyasa, kuma ‘yar rajin kare hakkin dan Adam a Nijeriya, a yayin da matasan Sharifai suka ziyarceta a ranar wata Asabar 9/7/2016, ta yi kira da cewa: “Kirana ga almajiran Shaikh Zakzaky shi ne; Ku yada manufar Shaikh Zakzaky a ko ina a duniya, domin Shaikh ne kadai ya damu da halin da kasar nan take ciki, kuma shi ne kadai zai iya kawo adalci ga al’ummar nan!”
Shaikh Ibraheem Zakzaky na da mata daya ce, Malama Zeenah Ibrahim. Kuma Allah ya azurta su da samun ‘ya’ya guda tara; 7 maza da 2 mata, wanda kuma shida daga cikin mazajen sun samu Shahada a waki’ar Quds ta shekarar 2014 da kuma waki’ar Buhari ta shekarar 2015 a Zariya.
An rubuta littafai da dama a kan tarihin Shaikh Zakzaky da da’awarsa, daga ciki akwai littafan da Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky ta wallafa da suka hada da; Muhimman Ranaku 200 A Tarihin Harkar Musulunci, Da’awar Harkar Musulunci, Haramtacciyar Shari’a Ga Shaikh Zakzaky, Harkar Musulunci, da sauran littafai, wadanda yawancin bayanan da ke cikin wannan rubutun daga cikinsu na samo.
Tun bayan da Shaikh Zakzaky ya fito daga kamun Buhari a ranar 29/7/2021, Jagoran na zaune a gidansa da ke Abuja, inda yake samun baki daban-daban maziyarta daga almajiransa da magoya bayansa da kuma sauran al’ummar kasa. A yayin da tuni aka mai da mafi yawan manyan tarurrukan Harkar Musulunci suka koma Abujan, bayan a baya a kan yi su a Zariya ne.
Muna addu’ar Allah Ta’ala ya kara masa lafiya da tsawon kwana. Ya cika masa burinsa na ganin al’umma ta shiryu, addini ya kafu daram, ya yi iko da mu a doron kasa.
— Saifullahi M Kabir.
Muhdsaifu@gmail.com
15 Sha'aban 1444 (7/3/2023)

