Offline

MARTANI: Idan Nasiru Mahaukaci Ne Bai Kamata 'Yan Jihar Kaduna Su Zama Mahaukata Ba!

 


–Saifullahi M. Kabir


Kun san a shekarar 2007 tsohon Gwamnan jihar Sakkwato, Alu Wammako ya yi kamfen ma Sakkwatawa da zai kawar da Shi'a, bayan ya aza malamai sun rika aibata Shi'a da Shi'anci da nuna ta a matsayin wata annoba gare su, kai kace ita ce sanadiyyar talaucin da suke fama da ita. Alu ya yaki Shi'a, ya rusa Markaz din yan uwa na Sokoto, ya kashe mutane, ya kama fiye da 100 ya daure a Kurkuku, ya kona shaguna da gidajen yan uwa sama da 200.


Shikenan, ya yi iya kokarinsa, amma har yau ga Shi'a nan daram a Sokoto, sai ma karfi ta kara, Markaz din yan uwa na yanzu ta nunka wacce Alu ya rusa, yan uwa da karfinsu a Sokoto, arzikinsu ya ninninku, shi kuma ba abin da yake sai kara lalacewa da tabalbalewa, kuma akwai wannan bashin a kansa, zai biya ba makawa a yayin da Allah Ta'ala Ya masa kamun karshe!


Yanzu shi Gwamnan Kaduna, Nasiru Rufa'i wanda asali ba shirinsa bane Kisan Kiyashin Zariya, daga baya aka saka shi a cikin tsarin shima, amma sai ya yi kane-kane, yana kokarin nuna kamar wani tsarinsa ne, aikinsa ne, gudanarwarsa ce, har ma yana ganin kamar nasararsa ce. Wane uban mutum! Kai dai an saka ka a matsayin karen farauta, kuma ka taimaka wajen taya magidantanka aikin da suka kasa samun nasararsa tun a duniya, kuma akwai azaba mai narko a kanku a lahira. 


Aka ce min wai shi Rufa'i bayan duk irin ta'addancin da ya ma al'ummar jihar Kaduna na rusa gidajensu, kasuwanninsu, koran ma'aikatansu da wargaza mutuncin masarautunsu da takura musu da azabtar da su, da ciyo musu matsanancin bashi a jiharsu da raini da izgili da yake musu, amma wai ya rasa abin da zai ma wasu Malamansu kamfen sai da cewa ya yaƙi 'yan Shi'a, kuma yana son su zabi magajinsa Uba Sani, don ya cigaba da hana yan Shi'a sakewa a jihar Kaduna.


Shine Shi'a ne matsalar jihar Kaduna? Koran ma'aikata da ya yi ne maganin Shi'a ko rusa kasuwanni? Ko kara kudin makaranta ga Malamai? Ko jefa mutane a cikin matsanancin yanayi ne maganin Shi'a? Ku za ku zabi Uba sani ne don ya magance matsalarku ta hana abin da ake kira Shi'a? 


Shine yanzu haka ma mai aka fasa a Zaria da Kaduna na gwagwarmaya? Yana yi kamar bai san cewa ba Muzahara ko Munasabar da ba a yinta a Zariya da Kaduna har yanzu. Har suna kokarin hanawa ya gagare su. 


Kuma wa ke ta Zaria ko Kaduna, Gwagwarmayar dama ba ta gari ko jiha bace, ta kasa ce, to ta tare a cibiyar kasar baki daya.


Harkar Musulunci ta faro tun Rufa'i na yaro ƙarami, kuma za ta wanzu har bayan ran jikansa, lokacin ya jima a Jahannama InshaAllah.


Ya ragewa mutanen Kaduna, su fahimci cewa ba Shi'a ko Harkar Musulunci ce damuwarsu ko matsalarsu ba, in ma za ta zama musu matsala to afka mata da kashe rayukan da aka yi ba bisa hakki ba, shine zai iya zamewa jihar matsala da fuskantar fushin Allah Ta'ala, babu ta inda fada da wasu mutane da kashe su ba bisa hakki ba zai taimaki al'ummar jihar Kaduna.


Ku farka, ku nemi hakkinku ne da hakkin iyalanku da aka yi kokarin É—aiÉ—aitawa a hannun azzaluman mahukunta, kuma abin da ya fi shine ku amsa Da'awar mai kira zuwa ga komawa tsarin Allah Ta'ala da tabbatar da nizamin addini, wanda shine kadai tsarin da zai iya shimfida adalci ga kowa, ya tabbatar da masu gaskiya a kan kujerun rikon amanar al'umma da kiyaye mutuncinsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post