Offline

BAIWAR ALLAMAH A FAGEN BADA ILIMI.


  

Shamsudeen Hassan.

Daga cikin Baiwar da Allah ya yiwa Allamah Sayyid Al-zakzaky, wadda ita kadai ta isa hujjar gano cewa shi na dabam ne a cikin na dabam, itace yadda yake kwararre wajen zaben wane kalar Ilimi ne ya kamata a baiwa Dalibai,  da kuma wane kalar Jawabi ne ya kamata a yiwa masu saurare, sannan kuma a wane Lokaci. 


Haziqi ne wajen Magance Cututtukan Zukata, wadanda suke banbanata daga Mutum zuwa Mutum, wadanda suke bukatar Kwararrun Malaman Zukata kafin Magancesu. Kamar yadda Kwararren Likita yake Haziqi wajen Magance Cututtukan Zahiri, a fannin Likitanshi da ya Kware a Kai.. 


A wajen Karantarwa, baya gaggawar bayanin Ilimi, ko fanni,  domin kawai yana jin ya San fannin, kamar yadda sauran Malamai suke yi, sai dai idan bukatar haka ta kama, kuma zai baka ilimin ne dai-dai yanayinka da Bukatarka. 


Shi ba bawan Isdilahohi bane, balle  ciwon bayaninsu ya kamashi. Misali, Baya bayanin Ka'idojin Arabiyyah, Irinsu Nahwu Sarfu Balaga, sai idan ta kama Dole. Duk da ko cewa tuni  Kadaminsa yake a saman Tozonsu. 


Ya San Irfanun Nazari kamar yadda yake Dabbaqa Irfanin aiki. Amma ba kasafai kake jin yana bayanin Isdilahohin Arifai ba, sai a inda ya dace, ga wanda ya dace. 


Gangaran ne a Ma'aqulat, amma idan yana bayanin Manqulaat sai ka dauka ko cikin Mafarki bai taba haduwa da su ba. 


A fannin Tarihi ya hada biyu. Shi Historian ne, kima Historiographer, a lokaci guda kuma shi Historical Philosopher ne. Amma duk da haka yana bayanin Waqa'iqu na tarihi ta yadda Leburan da baya zuwa Aji zai ji kamar shi kadai ne ake yiwa bayanin. A Lokacin Farfesan Tarihi na gefe ya bude baki, ya zaro Idanu, yana mamakin wai wannan Mutum ne ko Mala'ikah. 


Wannan ne ya rudi wasu a shekarun baya suka dinga cewa ko fassara Ayah baya iya yi. Amma Lokacinda ya fara Tafsiri sai suka gano ashe sun banna Shekaru suna fassara Al-Qur'an Birkice, sun dade suna mashi yanka 'Yan Bori,  Maimakon na Musulunci. 


Ilimi cizon Mai shi yake idan bai fada ba. Isdilah Zungurar masaninsa yake idan bai Fedeshi ba. Amma shi Allah ya tsara masa Ilimomi ya Nazzama mashi Isdilaho, sai ya zamo yana Shayar da Mutane su Cibi-cibi, hade da Taqawa. 


Dubi sauran Malamai, komai Ikhlasin Mutum za ka tarar wani lokaci ya kucce yanata bayanin Ilmomin da basa da Amfani Muhallin da yake yinsu, ko kuma ga wadanda yake fadama su. 

Banda Allamah Al-zakzaky... 


Idan wannan ba shirin Allah da Kimtsawarshi da Kimsawarshi bace to mene ne kenan? 


Idan wannan ne bai isa hujja a kan cewa Su Malam Khasatul-Khuwwas bane to bamusan wace hujja mutum ke nema ba. Domin wannan baiwar masu ita a Tarihi daga Annabawa sai, Imamai, sai ko Mijadaddai na Addini, bana Mazhaba kawai ba. 

ٱرْجِعِ ٱلْبَصَرَ ÙƒَرَّتَÙŠْÙ†ِ ÙŠَنقَÙ„ِبْ Ø¥ِÙ„َÙŠْÙƒَ ٱلْبَصَرُ Ø®َاسِئًا ÙˆَÙ‡ُÙˆَ Ø­َسِيرٌ




https://t.me/Drshamsudden

Post a Comment

Previous Post Next Post