—Sheikh Ibraheem Zakzaky [H].
“Kuma wani abu ne da za asa rai yazo, harma in baizo ba ya kamata mu sama kanmu ayar tambaya, Anya ko akan tafarkin muke? tunda yake tafarkin wadanda ake jarabawa ne, Allah ta'ala ya jarabta magaba ta kuma zai jarabta wanda zasu zo daga baya, wannan lazim ne. Saboda haka Jarabawa dama abin da za'a sa raine. Amma jarabawo yinnan baza su Æ™ara mana komai ba sai ci gaba.”
“Saidai Kamar yadda mukan ce mishkilan jarabawa itace ba kowa ke ci ba, abin da muke jin tsoro kenan kada wata rana ayi bamu, mu faÉ—i jarabawa. Muna fatan Allah yasa mu hayike. Kar ya zama a gama maki ace to mu bamu hayike ba. Kaga wannan ya jaddada mana ba majal ne na yabo ba, kona yabon kaiba, ko na cewa wane ne yayi kaza, ko wane baiyi kaza ba. Majal ne na godiya ga Allah ta'ala.
—Sheikh Ibraheem Zakzaky [H], cikin jawabin sa yayin ganawa da wakilan 'yan uwa, domin taya al'ummar musulmi murnar haihuwar Imam Mahdi (AS) ranar 18-03-2022 a gidan sa dake Abuja Nigeriya.
