Offline

YADDA AKA GUDANAR DA ZAGAYEN MAULUDIN MANZON ALLAH (S) A GARIN KADUNA...



KD PRESS

Gamayyar ɗariƙun Ƙadiriyya da Tijjaniyya haɗi da ƴan'uwa Musulmi Almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) na garin Ƙaduna, sun gudanar da zagayen Mauludin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAWA) kamar yadda suka saba gudanarwa a duk shekara. Zagayen wanda aka fara shi da sanyin safiyar ranar Asabar 08 October, 2022, daidai da 12 ga watan Rabi'u Awwal Hijira na da shekera 1444AH.

A irin wannan rana ta 12 ga watan Rabi'ul Awwal ne mabiya ɗariƙun Sufaye suka yi imani da cewa rana ce da aka haifi fiyayyen halitta Manzon Allah (S), kasancewar ƴan'uwa musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) mutane ne masu nuna tsananin soyayya ga janibin Manzon Allah (S) ne ya sa su ma suke musharaka a irin wannan rana tare da sauran jami'a.


Zagayen Mauludin Manzon Allah (S) a garin Ƙaduna  yakan zo da abubuwa iri daban-daban na ban mamaki a duk shekara, inda mutane a cikin garin da wajen garin ke samun halartar zagayen Mauludin, cikin sababbin É—unkuna suna tafe suna rera waÆ™oÆ™in begen Manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka. Ƴan'uwa Musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) dai sun kasance cikin tsari da nizami a lokacin da ake gudanar da zagayen, su ma suna tafe suna rera waÆ™oÆ™in yabo ga fiyayyen halitta (S).


Matasa da yara ƴan Fudiyya ba a barsu a baya ba wurin taka faretin girmamawa ga Manzon Allah (S), haka kuma matasa sun taka slogans na baitocin waƙoƙi ga Manzon Allah (S). An fara Muzaharan ne daga Masallaci Shehu Dahiru usman Bauchi, har zuwa stediom,


Ga wasu daga cikin hotunan da muka É—auka a daidai lokacin da ake tsaka da gudanar da zagayen Mauludin.


Kaduna Press
8/10/2022

Post a Comment

Previous Post Next Post