Offline

WAFATIN SAYYIDA FAƊIMA ƳAR IMAM HUSAIN (A.S.)




 Ahaifi Sayyida Fadima ƴar Imam Hussaini (a.s) a shekara ta 40 bayan hijira a mafi ingancin zance , kuma mahaifiyarta ita ce Shahrbanu ‘yar Kisra Yazdajard (Mahaifiyar Imam Aliyu Zainul Abidin) . Ta auri ɗan baffanta Al-Hassan Al-Muthanna ɗan Imam Al-Hassan Al-Mujtaba ɗan Imam Ali da Sayyida Fatima (a.s) , wanda ya yi shahada a shekara ta 97 bayan hijira bayan Al-Walid bin Abdul-Malik ya shayar da shi guba, ta kuma kasance cikin baƙin ciki da yi masa kuka har Allah yayi wafatinta a ranar 4 ga watan Rabi’ul Awwal , shekara ta 110 bayan hijira, a wata ruwayar kuma aka ce a shekara ta 117 bayan hijira. An ce an binne ta (Rahimahallah ) a Masar, a wani ƙaulin an ce a Sham ne , wani kuma a Madina , amma yanzu haka akwai harami da masallacinta a Misra . Ta kasance tare da mahaifinta Imam Hussain (a.s.) a Karbala , kuma tana cikin matan da aka kamasu a matsayin ribattatun yaƙi, daga Karbala zuwa Kufa sannan Sham har zuwa Madina , Sayyida Fatima tana da huɗubobi shahararru da tayisu a Kufa da Sham , lokacin da ake yawo dasu gari-gari bayan kashe Imam Hussain (a.s.) . An fuskanci tuhume-tuhume da kuma murguɗa tarihin rayuwar Sayyida Fatima bint Al-Hussain, inda aka ce bayan rasuwar mijinta Al-Hasan Al-Muthanna ta auri Abdullahi bin Amr bin Othman bin Affan, wanda ya rasu a shekara ta 96 bayan hijira a Masar. Bayansa kuma suna da’awar cewa ta auri Abdurrahman bn Dahhak al-Fihri, Gwamnan Yazid bn Abdil-Malik a garin madina a shekara (101-104) bayan hijira . Sai dai duk wannan ƙarairayi ne da basu da asali , maƙiya ne suka ƙirƙiresu , wanda dalilai masu tarin yawa sun tabbatar da rashin ingancin hakan cikin abinda malamai sukayi rubuce-rubuce game da rayuwarta mai Akbarka . عليها الصلاة والسلام والرحمة ..... ✍️ Ibnul Marja'iyya Al-Abdul Faneey Al-kanaweey

Post a Comment

Previous Post Next Post