Ghassan Daghlas jami’in Falasdinu da ke sa ido kan ayyukan ‘yan mulkin mallaka na Isra’ila ba bisa ka’ida ba a yankin arewa maso yammacin gabar kogin Jordan, ya ce ‘yan mulkin mallaka sun zo da Bulldozer (Motar Rusau) masu yawa tare da rushewa da tunbuke gonakin Palasdinawa da ke kusa da haramtacciyar kasar Isra’ila.
Daghlas ya kara da cewa filayen wani bangare ne na kauyuka da garuruwa shida a kudancin Nablus kuma suna fuskantar karuwar take hakki na Isra'ila a daidai lokacin da ake ci gaba da gine-gine da fadada haramtacciyar kasar.
An kewaye filayen kuma an ware su, kuma an hana masu gonakin su shiga.
A wani labarin kuma, sojojin Isra'ila sun rufe shingayen sojojin na Huwwara da Beit Furik tare da hana Falasdinawa shiga Nablus, bayan da suka tilastawa motocin da mazauna wurin ficewa.
Dukkanin yankunan da Isra'ila ta yi wa mulkin mallaka a Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye da suka hada da na Gabashin Kudus da kewaye, haramtattu ne a karkashin dokokin kasa da kasa, Yarjejeniyar Geneva ta hudu baya ga kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitin Tsaro daban-daban. Sun kuma zama laifukan yaki a karkashin dokokin kasa da kasa.
Mataki na 49 na Yarjejeniyar Geneva ta Hudu ya bayyana cewa: "Mallakar da ke mulki ba za ta kori ko kuma mika wani bangare na farar hularta zuwa yankin da ta mamaye ba." Har ila yau, ta haramta “canja wuri na mutum É—aya ko na jama'a, da kuma korar mutane masu kariya daga yankin da aka mamaye”.
Source: IMEMC